Zaben Edo: PDP ta yi fallasa, ta zargi APC da yunkurin sauya sakamakon zabe

Zaben Edo: PDP ta yi fallasa, ta zargi APC da yunkurin sauya sakamakon zabe

- Sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya sanar da kokarin murde musu zabe

- Kamar yadda ya fitar a wata takarda, ya ce sun gano cewa ana kokarin yin aringizon kuri'u

- Ya ce daga sassan da rafuka suke na jihar da arewacinta ake son sauya alkalumman domin APC

Jam'iyyar PDP ta zargi cewa ana takurawa tare da tsananta wa hukumar zabe mai zaman kanta don juya sakamakon zabukan da ke isowa na gwamnan jihar Edo.

Duk da wannan ikirarin, Premium Times ta tabbatar da cewa bata da wata shaida da ke bayyana hakan.

A wata takarda da sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya fitar a ranar Asabar, jam'iyyar ta zargi cewa tana sane da takurar da hukumar ke fuskanta domin sauya alkalumman zabe a yankunan ruwa na jihar domin APC ta lashe zaben.

"Jam'iyyar PDP ta gano cewa, shafin yanar gizo na INEC wanda ake sako sakamakon zabe yana cigaba da tabarbarewa.

"An sanar da mu cewa ana matsantawa shugaban INEC daga APC a kan cewa ya aminta da aringizon kuri'u domin samun nasarar APC

"Mun sake samun labaran cewa za a sauya sakamakon Fugar tare da na sauran kananan hukumomi da ke arewacin jihar Edo.

"Muna kira ga shugaban hukumar INEC ta kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, da kada ya amince da wannan tirsasawar ko saboda hadin kai tare da zaman lafiya a kasar nan.

"Muna da sakamakon zabuka daga rumfunan zabe, kuma muna kira ga INEC da ta karba sakamakon da jami'anta kadai suka fitar.

“Muna kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da lura da shafin yanar gizo na INEC domin tabbatar da an bi ra'ayin jama'ar jihar Edo," takardar tace.

KU KARANTA: Zaben Edo: Tattara komatsanka ka bar jihar Edo - 'Yan sanda ga Wike

Zaben Edo: PDP ta yi fallasa, ta zargi APC da yunkurin sauya sakamakon zabe
Zaben Edo: PDP ta yi fallasa, ta zargi APC da yunkurin sauya sakamakon zabe. Hoto daga Premium Times
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yar uwar Boko Haram: Yadda rundunar soji ke matsanta wa Darul Salam

An yi zaben gwamnan jihar Edo a fadin kananan hukumomi 18 na jihar kuma an kammala. A halin yanzu ana cigaba da tattara sakamakon zabe a hedkwatar INEC da ke Benin.

Jam'iyyun siyasa 14 suka fito takarar, amma jam'iyyu biyu da 'yan takararsu ne kadai suke kan gaba.

Gwamna Godwin Obaseki shine dan takarar jam'iyyar PDP yayin da Osagie Ize-Iyamu dan takarar jam'iyyar APC.

A wani labari na daban, sakamakon da hukumar gudanar da zaben kasan watau INEC ya nuna cewa gwamnan jihar Edo mai ci yanzu, Godwin Obaseki, ne kan gaba da tazarar kuri'u kimanin dubu dari tsakaninsa da na biye da shi, Osagie Ize-Iyamu, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Legit.ng ta ruwaito muku cewa an gudanar da zaben gwamnan jihar ne ranar Asabar, 19 ga Satumba, kuma hukumar INEC na tattara sakamakon yanzu.

Channels TV ta ruwaito cewa an sanar da sakamakon kananan hukumomi 13 kuma Obaseki ya lashe guda 11 yayinda abokin hamayyarsa ya ci biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng