Sultan Sa'ad Abubakar III ya nada sabbin hakimai 15 a Sokoto

Sultan Sa'ad Abubakar III ya nada sabbin hakimai 15 a Sokoto

- Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya nada sabbin hakimai 15 a jihar Sokoto

- Sarkin ya nada su ne sakamakon rasuwar tsaffin hakiman da ke jagoranci a garuruwan 15

- Cikin sabbin hakiman da aka yi wa nadin akwai mahaifin mataimakin gwamnan Sokoto, Muhammad Dan'iya

Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III, a ranar Asabar ya nada sabbin hakaimai 15 a Jihar Sokoto.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ta ruwaito cewa anyi nadin ne bayan rasuwar hakiman da ke shugabancin garurruwan.

DUBA WANNAN: Zaben Edo: 'Yan daban da ke yi wa PDP aiki sun yiwa matar shugaban jam'iyyar mu duka - APC (Hotuna)

Sultan ya nada hakimai 15 a Sokoto
Sultan ya nada hakimai 15 a Sokoto
Source: Twitter

Sarkin musulmin ya tayya sabbin hakiman murna kuma ya bukaci su tabbatar sun yiwa garurruwansu wakilci mai kyau a majalisar sarkin musulmin.

"Nadin da aka yi muku karin nauyi ne da kuma dama domin ku yi wa garurruwan ku hidima, saboda haka ina kira gare ku ku mayar da hankali domin tabbatar da kawo cigaban da al'umma.

KU KARANTA: Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

"Ana sa ran ku cigaba da aiki tare da mutanen ku domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai mai dorewa a jihar," in ji shi.

Kazalika, Sultan din ya yi wa sabbin hakiman addu'a sannan ya yi wa kasa addu'ar samun zaman lafiya da cigaba.

NAN ta ruwaito cewa wadanda aka nada a matsayin hakiman sun hada da hakimin Kware, Muhammad Dan'iya, mahaifin mataimakin gwamnan jihar Sokoto da Mai shari'a Mohammed Tsamiya a matsayin hakimin Tsamiya da sauransu.

A wani labarin daban, An nada tsohon jami'in tuntuba na Majalisar Tarayya, Sanata Muhammad Abba-Aji a matsayin Sakataren kungiyar gwamnonin yankin Arewa ta Gabas, NEGF.

Abba-Aji ya rike mukamin jami'in tuntuba a majalisar tarayya a zamanin mulkin shugaban kasa Umaru Yar'adua da Goodluck Jonathan.

An fara nada shi mukamin na shekaru biyu sannan aka sabunta nadinsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mallam Isa Gusau, Kakakin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum wanda shine shugaban kungiyar ya ce an sanar da nadin Abba-Aji ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watar 15 ga watan Satumban 2020 mai dauke da sa hannun Zulum.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel