Zaben Edo: Tattara komatsanka ka bar jihar Edo - 'Yan sanda ga Wike
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana mamakinsa a kan abinda sifeta janar na 'yan sandan Najeriya yayi masa
- Kamar yadda Gwamnan yace, babban dan sandan Najeriyan ya bashi umarnin barin jihar Edo da gaggawa
- Ya tabbatar da cewa yana nan daram, babu inda zai je tunda gwamnonin APC suna walwalarsu a cikin jiharsa
Gwamna Wike na jihar Ribas a daren Juma'a ya bayyana mamakinsa a kan tambayar da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, yayi masa.
Wike ya sanar da cewa babban dan sandan Najeriyan ya bukacesa da ya tattara komatsansa ya bar jihar Edo duk da yace ba a dauka wannan matakin a kan sauran gwamnonin APC da suka ziyarci jihar ba.
Gwamnan ya ce ya sanar da sifeta din 'yan sandan cewa, ya ziyarci jihar domin duba yadda zaben da za'ayi ranar Asabar zai tafi.
"Sifeta janar din ya bukace ni da in gaggauta barin jihar. Na tambayesa dalili. Gwamnan jihar Kano da na Imo duk suna garin. A kan mene zai ce ni kadai in bar jihar? Ban taba ganin abu kamar haka ba," Wike yace.
Ya kara da cewa, zai cigaba da zama a Benin City yana lura da zaben har sai an kammala, Wike ya sanar da Channels TV.
Kafin Wike ya sanar da hakan, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya sanar da manema labarai cewa 'yan sanda na cin zarafi tare da firgita gwamnonin PDP a Edo, yayin da na APC ke walwalar da suke so.
KU KARANTA: Hotuna: INEC ta kai kayayyakin bukata na zaben jihar Edo
KU KARANTA: 'Yar uwar Boko Haram: Yadda rundunar soji ke matsanta wa Darul Salam
A wani labari na daban, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta na kuka kan zoben da jami'an hukumar yan sanda suka yiwa masaukin gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a Benin, babbar birnin jihar Edo.
Wike, wanda shine shugaban yakin neman zaben gwamnan jihar Edo na jam'iyyar PDP, ya dira jihar yayinda ake shirin zaben gobe.
A jawabin da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Rivers, Akawor Desmond, ya saki, ya ce kimanin yan sanda 300 sun zagaye masaukin da gwamnan yake zaune.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng