Zaben Edo: Yadda dan sanda ya nemi in bashi toshiyar baki - Mai sa ido kan zabe

Zaben Edo: Yadda dan sanda ya nemi in bashi toshiyar baki - Mai sa ido kan zabe

- Wani jami'in sa ido a kan zabe daga cibiyar 'yan jarida masu bincike na Premium Times, PTCIJ, ya ce wani dan sanda ya nemi toshiyar baki daga hannunsa

- Mai saka ido a kan zaben na PTCIJ ya ce 'yan sanda sun tare su ne a Okada Junction kan babban titin Sagamu -Ibadan suka hanna su wucewa duk da ya nuna katin shaidan aikinsa

- Ya ce dan sandan ya ajiye su na mintuna masu yawa bayan musu tambayoyi daga karshe ya nemi su bashi rabonsa ma'ana toshiyar baki kafin ya bari su koma inda suka fito

Wani dan sanda a yayin zaben gwamnan jihar Edo na shekarar 2020 ya nemi toshiyar baki daga hannun jami'in sa ido a kan zabe na Premium Times a ranar Asabar.

Dan sandan da aka tura ya yi aiki a Okada Junction da ke kan babban titin Sagamu - Ibadan ya tsayar da dan jaridar ya hana shi wucewa duk da ya nuna masa katin shaidar aikinsa.

Zaben Edo: Yadda dan sanda ya nemi in bashi toshiyar baki - Mai sa ido kan zabe
Zaben Edo: Yadda dan sanda ya nemi in bashi toshiyar baki - Mai sa ido kan zabe
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun afka wurin shaƙatawa a Kogi, sun kashe mutum ɗaya sun raunta da dama

"An tsayar da ni a Okada Junction (kan babban titin Sagamu-Ibadan) kuma an hana ni in wuce in tafi mazabun Ofunmwegbe da Okada East.

"Na nuna wa dan sandan katin shaidan aiki na amma ya ce dole sai dai in tsaya a rumfar zabe daya tunda ba ni da motar aiki ko na wata hukuma.

"Bayan fiye da mintuna biyar, ya ce ba zan iya komawa inda na fito ba. Na yi tunani na wasu mintuna sai na kira shugabanni na. Sun shawarce ni in koma Okada West.

KU KARANTA: Kano: 'Yan sanda sun kama matar da ta kashe ɗan kishiyarta

"Na sauka daga motar da na ke domin in yi wa shugaban su a wurin bayanin abinda ke faruwa."

A cewar mai saka ido kan zaben, dan sandan ta tambaye shi inda ya samo motar.

"Na amsa masa, 'Hayar ta na yi'. Ya sake tambaya, 'na wa?' na amsa masa 'N15,000.' Daga nan sai ya tambayi in bashi nashi kason (toshiyar baki) ya umurci daya daga cikin yaransa ya karbo daga hannun direba na.

"Na kira shugabanni na domin in fada musu abinda ke faruwa yayin da shi kuma direba na ya ke magana da dayan dan sandan da aka ce ya karbo toshiyar bakin a hannunsa. Da na koma mota sai dan sandan da aka ce ya karbi toshiyar bakin ya ce muna iya tafiya. Da muka tada mota za mu wuce shugaban 'yan sandan sai ya tambaye ni, 'ka gan shi' na amsa 'Eh' don na san da sun bata mana lokaci idan na ce a'a."

Na tambayi direba na ko ya bashi kudi sai ya ce a'a.

Jam'iyyun siyasa 14 ne suka gabatar da 'yan takara a zaben gwamnan na Edo ciki har da 'yan takarar da suka fi fice biyu, Osagie Ize-Iyamu na APC da Gwamna mai ci Godwin Obaseki na PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel