Zaben Edo: 'Yan daban PDP suna firgita masu zabe da ma'aikatan INEC - APC

Zaben Edo: 'Yan daban PDP suna firgita masu zabe da ma'aikatan INEC - APC

- Jam'iyyar APC ta koka kan cewa jam'iyyar PDP tana amfani da 'yan daba wurin razana masu zabe da ma'aikatan INEC a Edo

- Kakakin kwamitin yakin neman zaben gwamna na dan takarar APC, Prince John Maiyaki ne ya yi wannan zargin cikin wata sanarwa da ya fitar

- John Maiyaki ya lissafa kananan hukumomi da dama da rumfunan zabe inda ya yi ikirarin 'yan daban PDP sun tarwatsa masu zabe da ma'aikatan INEC musamman wuraren da APC ke samun galaba

Jam'iyyar All Progressives Party, APC, ta bayyana damuwar ta a kan yiwuwar barkewar rikici a Urhonigbe da Owan ta Yamma inda ta ce zargin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP na yi wa masu zabe da ma'aikatan INEC barazana.

Kakakin yakin neman zaben gwamnan APC na Edo, Prince John Mayaki ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Zaben Edo: 'Yan daban PDP suna firgita masu zabe da ma'aikatan INEC - APC
Zaben Edo: 'Yan daban PDP suna firgita masu zabe da ma'aikatan INEC - APC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

A martanin da ya mayar cikin gaggawa, Sakataren watsa labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya ce jam'iyyar ta APC kawai fargaba ta ke yi ganin ta fara shan kaye.

Tunda farko Tukumar zabe mai zaman kanta INEC ta tabbatar cewa an yi harbe harben bindiga a Urhonigbe kuma ta ce tana aiki tare da jami'an tsaro domin hana tashin hankali.

A cikin sanarwarsa, Maiyaki ya ce, "Kamar yadda ta faru a Uhunmwode gunduma ta 2 mazaba ta 6, wakilan PDP sun fara tada fitina a Urhonigbe ta Arewa gunduma ta 7 da ke makarantar Frimare na Idunmwongo da ke karamar hukumar Orhionmwon inda ma'aikatan zabe suka tsere saboda harbe-harben bindiga da 'yan daban PDP ke yi.

"Kazalika, 'yan bindigan PDP sun kwace iko a akwatin zaben su Pius Odubu inda APC ke da magoya baya masu yawa. Sannan a Owan ta Yamma, gunduma ta 1, akwatin zabe na 3 da 4, 'yan daban PDP sun fara korar kowa saboda APC ne ke kan gaba a wuraren.

KU KARANTA: Da duminsa: An harbi mutum daya a Edo

"Haka zancen ya ke a karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas, inda PDP ta tarwatsa zabe wadda hakan ka iya janyo rikici."

"Dukkan wadannan abubuwan suna faruwa ne duk da cewa akwai 'yan sanda masu yawa a rumfunan zabe a jihar," in ji shi.

Mayaki ya kuma kara da cewa, 'yan daban na PDP sun kori masu zabe a mazaba ta 4 da ke karamar hukumar Oredo inda dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, Gwamna Godwin Obaseki ya jefa kuri'arsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: