Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana

Al'ummar jihar Edo a yau Asabar, 19 ga watan Satumba, sun fara shirin zaben wanda zai rike ragamar mulkin jihar.

Akwai yan takaran kujeran gwamnan 14 dake fafataw,a amma ana tunanin gwamnan da ke kai yanzu, Godwin Obaseki na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Osagie Ize-Iyamu na All Progressives Congress (APC) ne wadanda zasu fafata.

Alkaluman hukumar zabe INEC sun nuna cewa mutane milyan 1.72 ne zasu iya kada kuri'a yayinda 483,796 ba zasu iya ba saboda basu karbi katin zabensu ba.

Wakilan Legit.ng na jihar Edo yanzu haka domin kawo muku rahotanni kai tsaye game yadda abubuwa ke gudana

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Asali: UGC

Jami'an tsaro sun mamaye ofishin INEC na jihar Edo

An samu tsanantar tsaro a babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Edo da ke Benin City.

Kamar yadda The Punch ta wallafa, an ga jami'an tsaro sun mamaye dukkan farfajiyar ofishin.

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

An damke wasu gardawa uku da suke kokarin amfani da katin zaben bogi wajen zabe

An damke wasu matasa uku a PU011 PU 011(Iyowa, Ezuwarha Primary School) Ward 04(Adolor) suna amfani da katin zaben bogi wajen kada kuri'a

Daga #TheElectionProject #EdoDecides

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Asali: Twitter

Rikici ya barke a rumfar zaben Obaseki a kan siyen kuri'a

Siyen kuri'u ya mamaye dukkan makarantar firamare Emokpae da ke kan titin Missin, inda Gwamna Obaseki ya kada kuri'a.

Wasu fusatattun jama'a suna ta zanga-zanga a kan wannan cigaban.

Wannan shine abinda ke faruwa tsakanin jam'iyyun siyasa manya biyu. Wani mai kada kuri'a wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce zai amshe kudaden tare da saka wa wanda yake so kuri'a.

Bidiyon jirgin saman sojin Najeriya yana kaiwa da kawowa yayin da ake zabe

Philip Shaibu, mataimakin Obaseki yayin da yek kada kuri'a

Mataimakin gwamnann jihar Edo, Philip Shaibu, yayin da yake kada kuri'arsa a gunduma ta 11, rumfa ta biyar.

Shaibu ya kasance na hannun daman Godwin Obaseki a dukkan fadi-tashin da suka shiga kafin zaben.

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Gwamna Obaseki ya isa rumfar zabe, ya shiga layin kada kuri'a

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya isa rumfar zabensa domin kada kuri'a. Ya isa rumfar zaben tare da hadimansa inda aka fara tantancesa.

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana. Hoto daga Olubiyo Samuel
Asali: Original

Rikici ya barke a rumfar zaben Gwamna Obaseki

Rikici ya barke a rumfar zabe ta 019 da ke gunduma ta 4 a karamar hukumar Oredo ta jihar Edo.

Hakan ya faru bayan isar Gwamna Obaseki, kuma dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP.

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Asali: Original

Tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomole ya shiga layi, zai kada kuri'arsa

Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, ya shiga layi yanzu yana shirin kada kuri'arsa a rumfar zabensa dake Iyamho, karamar hukumar Estako

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Tshon gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Asali: Twitter

Wakilan PDP sun fara siyan kuri'a a karamar hukumar hukumar Egueben

Wakilan jam'iyyar PDP da ke gunduma ta 6, rumfar zabe ta 6 a karamar hukumar Igueben, sun fara siyan kuri'u.

An dauka hotonsu yayin da suke jan masu zabe bayan azuzuwa inda suke biyansu kudi, The Cable ta tabbatar.

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

Dan takaran jam'iyyar APC, Osaze Ize-Iyamu ya kara kuri'arsa

Daya daga cikin manyan yan takara a zaben yau, Fasto Osaze Ize-Iyamu ya kada kuri'arsa a rumfar zabensa dake

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Asali: Twitter

'Yan sanda sun tsare motoci, sun hana kaiwa da kawowar ababen hawa

Kwamishinan 'yan sandan jihar Edo, Lafimihan Adeoye, ya jagorancin 'yan sanda masu tarin yawa inda suka tsare motoci da ke tunkarar Ugbor a Benin City.

Idan za mu tuna, an hana walwalar ababen hawa a jihar domin dakile duk wani yunkurin 'yan daban siyasa da sauran masu tada zaune tsaye da ke kokarin hana zaben cikin lumana.

Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana
Kai tsaye: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana. Hoto daga Samuel Olubiyo
Asali: Original

An nemi takardar sakamakon zabe an rasa a Owan West dake gundumar ta 4, rumfa ta 17 (Daily Trust)

Ma'aikatan INEC sun fara isa rumfunan zabe

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng