'Yar uwar Boko Haram: Yadda rundunar soji ke matsanta wa Darul Salam

'Yar uwar Boko Haram: Yadda rundunar soji ke matsanta wa Darul Salam

- Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Manjo janar John Enenche, ya ce suna cigaba da matsantawa kungiyar Darul-Salam

- Kamar yadda rundunar ta ce, tana aiki da bayanan sirri inda har ta bankado wasu iyalai 290 da sansaninsu a Kogi da Nasarawa

- Enenche ya tabbatar da cewa nan babu dadewa kungiyar za ta zama tarihi domin kuwa akwai manyan alamu da ke nuna haka

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana sake matsanta wa Darul-Salam domin tabbatar da cewa duk wata barazana daga kungiyar ta kaura, Daily Trust ta tabbatar.

Shugaban fannin yada labarai na tsaro, Manjo janar John Enenche, ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyi daga manema labarai yayin zantawar mako-mako a kan ayyukan rundunar a Abuja.

Rundunar sojin ta bankado wasu iyalai 290 daga kungiyar Darul-Salam tare da sansaninsu da maboyarsu da ke Koton Karfe a jihar Kogi da wasu sassa na jihar Nasarawa.

Sun kai samamen ne bayan wasu mutum 410 sun mika kansu daga kungiyar a Toto da ke jihar Nasarawa.

Enenche ya ce, "Zan iya tabbatar muku da cewa nan babu dadewa kungiyar za ta yi layar zana. Muna cigaba da matsanta musu a kowanne fanni kuma muna samun bayanai a kansu.

"Ba da kai muke yin komai ba saboda kungiyar ta kafu ne sakamakon wani tunani na daban. Babban abinda ke da wuyar tafiya shine tunanin jama'a."

Tun farko, ya ce a kokarin kawo karshen ta'addanci a yankin arewa maso gabas, rundunar Operation Hadarin Daji ta cigaba da samun jerin nasarori a kan 'yan bindigar daji.

Ya ce a cikin lokacin, rundunar Operation SAHEL SANITY yayin aiki da bayanan sirri sun kama wani dilan makamai mai suna Usman Ibrahim daga Ryom a karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato.

Wanda ake zargin an kama shi da carbin harsasai 890 mai tsawon 7.62mm wanda ya boye shi a abun hawansa.

Sauran abubuwa da aka samu a wurinsa sun hada da wuka, bindigar fiston, katin shaida na dan sanda da N2,230,000.

Ya ce binciken farko ya bayyana cewa wanda ake zargin ke samarwa 'yan bindiga makamai a yankin arewa maso yamma.

KU KARANTA: Boko Haram: Dahiru Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa

'Yar uwar Boko Haram: Yadda rundunar soji ke matsanta wa Darul Salam
'Yar uwar Boko Haram: Yadda rundunar soji ke matsanta wa Darul Salam. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Cutata aka yi, ashe tana da 'ya'ya uku na aureta - Magidanci ya sanar da kotu

A wani labari na daban, Dakarun ‘yan sandan Najeriya sun ce an harbe wasu ma’aurata a garin Miyango da ke karamar hukumar Bassa a Filato.

‘Yan sanda sun ce wasu miyagun ‘yan bindiga da ba a sansu ba ne su ka yi samame a cikin daji, su ka kashe ma’auratan. Wannan lamari maras dadi ya faru ne a ranar Juma’ar da ta wuce da kimanin karfe 7:00 na yamma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel