Rundunar 'yan sanda ta tura jami'an da za su share cibiyoyin tattara sakamako, kada kuri'a

Rundunar 'yan sanda ta tura jami'an da za su share cibiyoyin tattara sakamako, kada kuri'a

- A gobe, Asabar, 19 ga watan Satumba, jama'ar jihar Edo za su fita domin kada kuri'unsu a zaben kujerar gwamna

- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa za ta tura jami'anta 31,000 a jihar Edo, domin kare ma'aikatan zabe da kayan zabe

- Daga cikin dalilan tura jami'an, a cewar Sifeta Janar na rundunar, Mohammed Adamu, akwai tabbatar da doka da yin zaben cikin lumana

A yayin da jama'ar jihar Edo ke shirin fita domin kada kuri'unsu a zaben gwamna na ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, rundunar 'yan sanda ta shiga na ta shirin.

A yau, Juma'a, ne rundunar 'yan sanda ta tura jami'anta da ke da kwarewa a kan bama-bamai da abubuwa masu fashewa (IEDs) zuwa cibiyoyin kada kuri'a da tattara sakamako domin su sharesu.

A cewar, Adeleye Oyebade, babban mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda (DIG) mai kula da tsaro yayin zaben Edo, an tura jami'an na musamman zuwa kowanne lungu da sako na jihar.

Yayin ganawarsa da manema labarai a hedikwatar rundunar 'yan sanda a Benin, Oyebade ya ce aiki da kwararrun jami'an ya zama wajibi domin kare faruwar abubuwan da ba a yi zato ba.

KARANTA: Yakin neman zabe: Atiku ya mayar da martani bayan sakon faifan bidiyon Tinubu a kan zaben Edo

DIG Oyebade ya ce rundunar 'yan sanda ta shafe watanni ta na shiri a kan zaben jihar Edo.

Ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda za su bayar da tsaro ta kowanne bangare domin ganin cewa an gudanar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.

"Mun saka yiwuwar samun sinadarai ma su fashewa (IEDs) a cikin tsarin aikinmu, a saboda haka akwai bukatar mu dauki matakan kiyayewa.

"Wannan zabe ne mai matukar muhimmanci, mun san cewa za a iya amfani da batagari daga makwabtan jihohi domin haddasa fitina. Mu kam a shirye mu ke ta kowanne bangare," cewar DIG Oyebade.

Rundunar 'yan sanda ta tura jami'an da za su share cibiyoyin tattara sakamako, kada kuri'a
Isar muhimman kayan aikin zaben jihar Edo
Source: Twitter

A ranar Talata ne Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya bayyana cewa za a tura jami'an 'yan sanda 31,000 zuwa jihar Edo domin kare ma'aikatan zabe, kayan zabe, da kuma tabbatar da doka.

"Mun tura jami'an 'yan sanda ma su yawa domin takawa duk wasu batagarin 'yan siyasa burki.

"Duk wanda ya sabawa doka ko kuma ya yi kokarin tayar da fitina za a gurfanar da shi.

KARANTA: Sunayensu: Hameed Ali ya nada DCGs 2, ACGs 5, ya sauya wa manyan jami'ai 5 wurin aiki

"Rundunar 'yan sanda za ta bayar da kariya ga wadanda su ka fita domin kada kuri'a cikin mutunci," kamar yadda IGP Adamu ya bayyana yayin taro da masu ruwa da tsaki a Benin ranar Litinin.

A Ranar Juma'a, 11 ga watan Satumba, IGP Adamu ya tura wasu manyan jami'an 'yan sanda zuwa jihar Edo domin su saka ido a kan zaben kujerar gwamna mai zuwa.

Babban mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda (DIG), Adeleye Olusola Oyebade, ne jagoran tawagar manyan jami'an da IGP Adamu ya tura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel