Bayan shekaru 14 ana gini da rikicin hana ginawa, an kammala ginin Masallacin Juma'ar farko a kasar Greece

Bayan shekaru 14 ana gini da rikicin hana ginawa, an kammala ginin Masallacin Juma'ar farko a kasar Greece

- Bayan shekara da shekaru, Musulman kasar Girka sun cimma babban burinsu

- Mabiya addinin Kiristan kasar sun hana ginin Masallacin saboda sune mafi yawa a kasar

- Firam Ministan kasar ya bada gudunmuwa wajen ganin an kammala ginin

An kammala ginin Masallacin Juma'ar farko a Athens, babbar birnin kasar Greece bayan shekaru 14 na gini da kuma rikice-rikice da wadanda suka lashi takobin ba za'a gina ba.

Yanzu za'a bude Masallacin a watan Oktoba, Daily Trust ta gano daga Euronews.

An jinkirta ginin Masallacin na tsawon lokaci sakamakon zanga-zangan da mabiya addinin Kirista ke yi kan ginin saboda sune mafi yawa a kasar Greece.

An yi ginin a fili eka 10 da coci ta bada kyauta Votanikos na birnin Athens.

Wani jami'in gwamnatin kasar ya bayyanawa jaridar Kathimerini cewa Firam Ministan kasar, Kiryakos Miçotakis a watan Yuni ya lashi takobin kammala ginin Masallacin.

Amma Masallacin mai fadin 850m2 kuma mai iya kwasan Masallata 350 bai da hatsumiya.

DUBA NAN: Ganduje, Yahaya Bello, da Oshiomole na cikin mutanen da Amurka ta haramtawa shiga kasarta

Bayan shekaru 14 ana gini da rikicin hana ginawa, an kammala ginin Masallacin Juma'ar farko a kasar Greece
Bayan shekaru 14 ana gini da rikicin hana ginawa, an kammala ginin Masallacin Juma'ar farko a kasar Greece
Source: Facebook

A bangare guda, Bayan shekaru 86 a matsayin gidan tarihi, musulmi za su cigaba da salla a Hagia Sophia da ke birnin Istanbul a watan Yuli, 2020.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan da wasu ƴan siyasa daga jam'iyyun Justice da Development da ma wasu ƴan siyasar za su halarci bikin buɗe masallacin.

Shugabanni da manyan baƙi daga ƙasashe kamar Azerbaijan da Qatar suma sun halarci bikin buɗe masallacin.

An bude taron da addu'o'i da kaburbura da sallatin Manzon Allah don gode wa Allah bisa wannan nasara da ya bawa al'ummar musulmin ƙasar.

DUBA WANNAN: Haramta shiga Amurkan kan magudi: Ba zan amince da hakan ba - Gwamnan Kogi ya mayarwa Amurka martani

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel