Yaran mu na shiga Boko Haram saboda rashin aikin yi - Gwamna Zulum

Yaran mu na shiga Boko Haram saboda rashin aikin yi - Gwamna Zulum

- Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya janyo hankalin 'yan majalisa game da halin da 'yan gudun hijira ke ciki a Borno

- Zulum ya bayyana cewa yara a jihar Borno suna shiga kungiyar ta'addanci na Boko Haram saboda babu ayyukan yi duba da cewa an raba su da gonakinsu

- Gwamnan ya yi gargadin cewa idan ba a dauki matakin taimaka musu na dindindin su koma gidajensu lafiya ba matsalar da ke tafe sai ta fi na yanzu

Yaran mu na shiga Boko Haram saboda rashin aikin yi - Gwamna Zulum
Yaran mu na shiga Boko Haram saboda rashin aikin yi - Gwamna Zulum. Hoto daga AFP
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama ɗan sanda bayan budurwarsa ta mutu a otel ɗin da suka kwana tare

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya yi gargadin cewa ana shigar da yara a Borno cikin kungiyar ta'addanci na Boko Haram.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tarbar wata kwamiti na mambobin 'yan majalisar wakilai a ofishinsa da ke Maiduguri a babban birnin jihar Borno.

Zulum ya ce shigar yaran cikin kungiyar ta Boko Haram na da alaka da rashin ayyukan yi a jihar, inda ya kuma ce akwai fiye da mutane 700,000 a sansanin 'yan gudun hijira a Monguna sannan akwai wasu 400,000 da aka raba su da gonakinsu.

KU KARANTA: Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

Ya ce;

"Hanyar daya da za a magance matsalar shine mu tabbatar mutanen mu sun koma gidajensu cikin mutunci. Idan ba a dauki mataki a kai ba ina tabbatar muku za mu fuskanci kallubalen da ya fi abinda muke fama da shi yanzu.

"Domin a yanzu 'yan ta'adda na shigar da yaran mu cikin kungiyarsu saboda karuwar rashin ayyukan yi."

Gwamnatin Jihar Borno ta bada shawarar cewa hanyar da za a magance wannan matsalar shine a mayar da hankali wurin daukan matakan taimaka wa mutanen na dindindin su samu su koma gidajensu lafiya a maimakon basu tallafi idan abu ya faru sai kuma a manta da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel