An kama ɗan sanda bayan budurwarsa ta mutu a otel ɗin da suka kwana tare

An kama ɗan sanda bayan budurwarsa ta mutu a otel ɗin da suka kwana tare

- An kama jami'in ɗan sanda a jihar Legas bayan budurwarsa ta mutu a ɗakin otel da suka kwana

- Rahotanni sun ce ɗan sandan ya shiga banɗaki ne sai ya fito ya tsinci budurwarsa fuskarta a kife a ƙasa

- Ƴan uwan budurwar sun ce ba su son a zurfafa bincike saboda ba su zargin kashe ta aka yi domin sun san da batun soyayyar su

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama wani jami'in ta mai muƙamin saja, Anthony Kachukwu bayan budurwarsa, Justina Omofuna ta mutu a wani ɗakin hotel a Surulere.

Punch Metro ta ruwaito cewa Anthony ya kai Justina hotel inda suka kwana tare amma da safe ta yanke jiki ta faɗi daga kujera ta suma.

An kama ɗan sanda bayan budurwarsa ta mutu a otel ɗin da suka kwana tare
An kama ɗan sanda bayan budurwarsa ta mutu a otel ɗin da suka kwana tare. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

A yayin faduwa daga kujerar ne ta buga kanta da ƙasa ta mutu sakamakon raunin da ta yi yayin faduwar.

DUBA WANNAN: Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

Wata majiya da ta yi magana da majiyar Legit.ng ta ce Anthony yana hira da Justina ne sai ya shiga banɗaki ya fito ya ga ta faɗi fuskarta a kife.

"Suna tare a ɗakin otel sai ya shiga banɗaki ita kuma tana zaune, da ya fito sai ya ga ta faɗi fuskarta a kife, da ya matsa kusa sai ya gano ta mutu," in ji majiyar.

Anthony ya kai kansa ofishin ƴan sanda da ke Surulere bayan anyi ƙoƙarin farfaɗo da ita amma ba ta farka ba.

Daga bisani an ɗauki gawar Justina daga otel ɗin an kai asibiti.

KU KARANTA: Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

Wani mazaunin unguwar da ya ce sunansa Adeoti ya ce iyalan Justina sun ce ba su son asibiti su binciki gawar don gano ainihin dalilin mutuwar ta domin ba su zargin akwai wata manaƙisa don sun san dama Anthony saurayinta na.

Amma duk da haka rundunar ƴan sanda ta cigaba da tsare shi ta ce zai fuskanci bincike daga ɓangaren rundunar.

Kakakin rundunar ƴan sandan Legas, Olamuyiwa Adejobi ya ce ba a tabbatar da ainihin dalilin mutuwar ta ba tunda ƴan uwanta sun ce a basu gawar ba su son a zurfafa bincike a kan lamarin.

A wani labarin daban, Jama'ar kauyen Unguwar Gambo da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina sun kashe wasu 'yan bindiga wadanda da ba a san yawansu ba.

Wasu mazauna yankin sun sanar da jaridar Daily Trust cewa, lamarin ya auku a ranar Lahadi yayin da daya daga cikin wadanda ake zargin dan bindiga ne ya bayyana sunan wadanda suke hada kai wurin aika-aikar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel