Na daukarwa Ubangiji alkawari, tazarcena bata cancanci zubar jini ba - Obaseki

Na daukarwa Ubangiji alkawari, tazarcena bata cancanci zubar jini ba - Obaseki

- Godwin Obaseki, dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin jam'iyyar PDP, ya ce ya dauka alkwarin ba za a yi rikici ba a zaben ranar Asabar

- Obaseki ya sanar da haka ne bayan azumin kwana daya da addu'o'i da suka yi na neman zaman lafiya da nasara

- Gwamnan mai fatan zarcewa, ya ce son tazarcensa bai kai ga son jama'ar jihar ba, don haka ba za a zubar da jini ba yayin zaben

Gwamnan jihar Edo kuma dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP, Godwin Obaseki, ya ce burinsa na tazarce bai zai sa ya bari jinin wani ya zuba ba, ya tabbatar da cewa zaben ranar Asabar a jihar zai kasance cike da zaman lafiya.

Jim kadan bayan jawabi a kan azumin kwana daya da addu'o'i domin fatan zabe cikin lumana, Obaseki ya yi kira ga duk wanda ya isa yin zabe da ya fito ba tare da tsoron tashin hankali ba.

Gwamnan wanda yace babu wata bukatar tashin hankali yayin zaben, ya jaddada cewa tare da goyon bayan jama'a da na mulkinsa, babu shakka jam'iyyarsa ce za ta yi nasara kamar yadda mai bashi shawara na musamman, Crusoe Osagie ya fitar.

Obaseki ya ce: "Coci wata madogara ce da ke tokare da mu, don haka ne yasa bani da wani tsoro. Ina daukar matakai kuma jama'a suna cewa ina da kwarin guiwa, ba ni bane, Ubangiji ne.

"Ina da coci da Ubangiji a tare da ni, mai zai bani tsoro?"

"Zabe yakamata ya zamo gasa ce inda jama'a ke siyar da bajintarsu. Jama'a ke fitowa da son ransu domin zaben wanda suke so. Bai kamata ya kasance tashin hankali ba.

“Bai kamata zabe ya zama wanda zamu zubar da jini ba saboda dole zai wuce. Idan ka mutu wurin zabe, a zabe na gaba ba wanda zai tuna da kai. Don haka babu bukatar tashin hankali," yace.

Gwamnan ya kara da cewa, "Abun takaici ne idan ka ga a yau kowa yana tsoro da tunanin za a yi rikici a zaben. Amma da izinin Ubangiji babu abinda zai faru. Duk za mu fito mu saka kuri'unmu kuma ba za a zubar da jini ba."

KU KARANTA: Shehu Sani ya caccaki Masari a kan bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da gonaki da zai yi

Na daukarwa Ubangiji alkawari, tazarcena bata cancanci zubar jini ba - Obaseki
Na daukarwa Ubangiji alkawari, tazarcena bata cancanci zubar jini ba - Obaseki. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dantabawa, makusancin Yari, ya yi magana a kan zarginsa da ake da taron sirri da 'yan bindiga

A wani labari na daban, kasa da sa'o'i 48 zuwa zaben gwamnoni na jihar Edo, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fara kai kayayyakin bukata na zaben jihar.

Gidan talabijin na Channels ya gano cewa, an ajiya kayayyaki masu matukar amfani na zaben a babban bankin Najeriya reshen jihar Edo da ke Benin City, inda suke ajiye kafin a fara rarrabewa.

An ga jami'an tsaro sun cika wurin daga rundunar sojin Najeriya, 'yan sanda da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng