Dantabawa, makusancin Yari, ya yi magana a kan zarginsa da ake da taron sirri da 'yan bindiga

Dantabawa, makusancin Yari, ya yi magana a kan zarginsa da ake da taron sirri da 'yan bindiga

- Wani makusancin tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya yi martani a kan kama shi da 'yan sanda suka yi

- An ranar Lahadi da ta gabata ne 'yan sanda suka kama Dantabawa sakamakon zarginsa da suke da taron sirri da wasu 'yan bindiga a gidansa

- Dantabwaa ya musanta hakan inda yace wakilan wadanda ambaliyar ruwa da ritsa da su ne tare da wasu abokansa da suka ziyarcesa

Abubakar Dantabawa, makusancin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya yi martani a kan kama shi da 'yan sanda suka yi a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, bayan bayanan sirri da aka samu daga CCTV da Gwamna Matawallle ya saka a babban birnin jihar Zamfara, an kama Dantabawa a ranar Lahadi, 13 ga watan Satumba, a kan zarginsa da ake yi da taron sirri da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne.

Amma kuma, yayin martani a kan batun a gidansa a ranar Alhamis, Dantabawa ya kwatanta kamen da 'yan sanda suka yi masa da maras tushe balle makama kuma cike da siyasa.

A yayin tabbatar da cewa ya yi wani taro a cikin gidansa, Dantabawa, ya musanta zargin da ake masa da taron da 'yan bindiga.

Ya ce wadanda suka halarci taron duk wakilai ne na wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa da su ne kuma ake kokarin basu taimako.

Ya ce: "Ina taro ne da wakilan jama'ar da ambaliyar ruwa ya ritsa da su. Wasu 'yan sanda sun shigo gidana wurin karfe 9 na dare inda suka cafke ni da wasu mutum 16.

"Abun mamakin shine yadda aka kama ni da wasu manyan sakatarorin gwamnatin jihar da wasu 'yan PDP tare da abokai na da suka zo ziyara.

“A yanzu su waye 'yan bindigar da ake zargin? Manyan sakatarorin gwamnatin?" ya tambaya.

KU KARANTA: Shehu Sani ya caccaki Masari a kan bai wa tubabbun 'yan bindiga gidaje da gonaki da zai yi

Dantabawa, makusancin Yari, ya yi magana a kan zarginsa da ake da taron sirri da 'yan bindiga
Dantabawa, makusancin Yari, ya yi magana a kan zarginsa da ake da taron sirri da 'yan bindiga. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Hamshakin mai kudi a duniya ya cimma burinshi na zama talaka kafin ya mutu, inda ya sadakar da duka dukiyar da ya mallaka

A wani labari na daban, daruruwan 'yan jam'iyyar APC a jihar Zamfara a ranar Lahadi sun tsinkayi hedkwatar 'yan sandan jihar da ke Gusau, inda suka mika bukatarsu ta sakin shugabansu, Abu Dan-Tabawa da sauransu.

An kama Dan-Tabawa sakamakon ganinsa da aka yi dumu-dumu yana taro da 'yan bindigar daji, kamar yadda hadimin gwamnan jihar Zamfara, Zailani Baffa ya sanar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel