Ka sauka daga mulki idan ba zaka iya bamu tsaro ba - Babban Limamin jami'ar Abuja ya caccaki Buhari

Ka sauka daga mulki idan ba zaka iya bamu tsaro ba - Babban Limamin jami'ar Abuja ya caccaki Buhari

- Malaman addinin Musulunci a sassan Najeriya na kira ga shugaba Buhari bisa halin da yan Najeriya ke ciki

- Akalla Malamai 5 yanzu sun aika budaddiyar wasika ga shugaban a watan nan

Babban limanin jami'ar Abuja (UniAbuja), Farfesa Taofiq AbdulAzeez, ya yi kira da shugaba Muhammadu Buhari, ya sauka daga karagar mulki idan ba zai iya bada tsaro ga mutanen Najeriya daga yan bindiga ba.

Shahrarren limamin ya bayyana hakan ne a hudubar Juma'ar da ya gabatar a Masallacin Jami'ar dake hanyar tashar jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja ranar Juma'ar da ta gabata.

Ya bayyana bacin ransa kan yadda rikice-rikice da hare-haren yan bindiga ya galabi Najeriya kuma gwamnati ta gaza yi komai.

Ya kara da cewa gwamnatin bata dauki hanyar gyara ba, ta saba alkawuran da ta yiwa yan najeriya kuma tana ciwo basussuka ba tare da jama'a na ganin ayyuka a kasa ba.

Ya kausasa kalamai kan matsalar tsaro inda yace, shine babban dalilin da ya aka kafa gwamnati; ta samawa al'ummarta tsaro.

"Mutane zasu iya hakuri kan hauhawar farashi, da wasu abubuwa da gwamnati ke yi amma idan babu tsari, babu zaman lafiya, da jin dadin rayuwa." Yace

Ya yi gargadin cewa idan ba'a magance matsalar rashin tsaro ba Najeriya ta dau hanyar halaka kanta da kanta.

Ka sauka daga mulki idan ba zaka iya bamu tsaro ba - Babban Limamin jami'ar Abuja ya caccaki Buhari
Buhari/Prof
Asali: Facebook

Jawabin Limamin ya biyo bayan bayanin gwamnatin Najeriya ta cewa yan ta'addan Boko Haram na shirin kai farmaki babbar birnin tarayya Abuja, da jihohin da ke makwabtaka.

Gwamnatin ta ce yan ta'addan na shirin kai hari ne wasu wurare na musamman a birnin tarayya kuma tuni sun kafa mabuya guda biyar a Abuja.

KARANTA WANNAN: Hukumar raya birnin tarayya ta fara rusa gidajen karuwai a Abuja

A cewar wata takardar da Kontrollan hukumar hana fasa kwabri wato kwastam, H.A Sabo, ya saki ranar 20 ga Agusta, 2020, ya bukaci dukkan hafsoshin su kasance cikin farga.

Takardar tace: "Labarin da Kontrola Janar na hukumar Kwastam ya samu ya nuna cewa akwai mabuyan yan ta'addan Boko Haram a ciki da wajen birnin tarayya Abuja."

"Karin bayani ya nuna cewa suna shirin kai hari wasu wurare cikin birnin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel