Wahalar man fetur ta tunkaro Abuja da sauran jihohin arewa

Wahalar man fetur ta tunkaro Abuja da sauran jihohin arewa

- A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur, lamarin da ya kara farashin litar man fetur a gidajen mai

- A yayin da har yanzu jama'a ke korafi a kan karin farashin mai, alamu na nuni da cew za a shiga wahalar man a arewacin Najeriya

- Otunba Salimon Oladiti, shugaban kungiyar direbobin dakon man fetur (PTD), ya bayyana dalilin mambobinsu na dakatar da aiki

Alamu sun nuna cewa Abuja da sauran jihohin arewa zasu fada cikin wahalar man fetur sakamakon dakatar da aiki da direbobin motocin dakon Mai su ka yi.

Kungiyar direbobin motocin dakon man fetur (PTD) ta umarci mambobinta su dakatar da safarar man fetur daga jihar Legas zuwa arewa har zuwa fitowar sanarwa ta gaba.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban PTD, Otunba Salimon Oladiti, an bayyana dalilin daukan wannan mataki.

DUBA WANNAN: Janye tallafin man fetur: Gwamnatin tarayya ta fadi ayyukan da zata yi da kudaden

PTD ta ce ta dauki wannan mataki ne sakamakon rufewa manyan motoci wasu muhimman hanyoyi a Minna, babban birnin jihar Neja.

Wahalar man fetur ta tunkaro Abuja da sauran jihohin arewa
Motar dakon man fetur
Source: Facebook

PTD ta ce hanyoyin da aka rufe suna sada manyan motoci da sauran jihohin arewacin Najeriya.

DUBA WANNAN: Nan da 2022 hawa mota mai amfani da fetur zai fi karfin talaka - shugaban DPR

Gwamnatin jihar Neja ta sanar da rufe hanyoyin ne daga daren ranar 15 ga watan Satumba, 2020.

"Mu na son yin amfani da wannan kafa domin sanar da jama'a cewa mambobinmu za su dakatar da dauko man fetur daga jihar Legas zuwa jihohin arewa daga ranar 17 ga watan Satumba.

"Mun dauki wannan mataki ne sakamakon rufewa manyan motoci wasu muhimman hanyoyi da gwamnatin jihar Neja ta yi.

"Sauran hanyoyin da zamu iya amfani dasu a halin yanzu a lalace suke.

"Na yi magana da ministan aiyuka ta hannun wani hadiminsa kuma ya bamu tabbacin cewa za su gyara hanyoyin, amma har yanzu shiru bayan sati biyu da maganarmu," a cewarsa.

A cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatare a ma'aikatar sufuri ta jihar Neja, Abdullahi Imam, gwamnatin jihar ta ce ta rufewa dukkan motoci hanyar shiga Minna.

Gwamnatin jihar ta ce ta dauki wannann mataki ne domin kare sauran hanyoyin jihar da manyan motoci su ka hanasu zama cikin yanayi mai kyau domin amfanin sauran ababen hawa da jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel