Hamshakin mai kudi a duniya ya cimma burinshi na zama talaka kafin ya mutu, inda ya sadakar da duka dukiyar da ya mallaka

Hamshakin mai kudi a duniya ya cimma burinshi na zama talaka kafin ya mutu, inda ya sadakar da duka dukiyar da ya mallaka

- Wani biloniya mai suna Charles "Chuck" Feeney ya cika burinshi na rayuwa kafin ya mutu, wanda shine ya tashi ya ganshi cikin talauci

- Feeney ya cika wannan buri nashi ne ta hanyar bayar da sama da dala biliyan takwas, sama da tiriliyan uku kenan a kudin Najeriya

- Mutumin ya ce yaji dadi sosai a lokacin da ya bayar da duka dukiyarshi kafin ya mutu

Biloniyan dan kasuwa Charles Chuck Feeney a karshe dai ya talauce bayan ya bayar da duka dukiyar shi sadaka tun yana raye.

Mutumin wanda ya samar da kamfanin Duty Free Shoppers, ya ce akwai dadi sosai idan ka bayar da dukiyar ka tun kana raye ba wai sai ka mutu ba.

Hamshakin mai kudi a duniya ya cimma burinshi na zama talaka kafin ya mutu, inda ya sadakar da duka dukiyar da ya mallaka
Charles Chuck Feeney | Photo credit: Graphic Online
Asali: UGC

A wani rahoto da Forbes ta fitar, sama da shekaru arba'in, Feeney ya sadaukar da sama da dala biliyan takwas, sama da naira tiriliyan uku kenan a kudin Najeriya.

KU KARANTA: Yadda wani biri ya saci wayar wani mutumi yaje ya dinga daukar hoto da bidiyo da ita

Ya bayyanawa Forbes cewa: "Mun koyi darasi da yawa. Zamu yi abu da yasha bamban, amma naji dadi sosai. Naji dadi dana nayi wannan abu tun ina raye."

Feeney ya nuna jin dadin shi ga mutanen da suka goyi bayan shi wajen bayar da duka abubuwan da ya mallaka. Inda yake rokar sauran mutane suyi koyi da shi.

KU KARANTA: Mutumin da yake acaba yana biyawa kanshi kudin makaranta ya zama dalibin da yafi kowa sakamako mai kyau

Ya ce: "Godiya ta ga wadanda suka goyi bayana da kuma wadanda suke tunanin bayarwa tun suna raye: Ku gwada zaku so hakan."

Yariman Dubai mai jiran Gado, Sheikh Hamdan bin Mohammed bin Rasha Al-Maktoum, ya nunawa duniya cewa ba komai bane idan ka zama mai adalci ga dabbobi.

Sheikh Mohammed ya dakata da amfani da motarsa mai kirar Mercedez Benz G-Wagon saboda ya samawa tsuntsayen guda biyu wajen da za suyi sheka.

Yariman ya daina amfani da wannan mota domin ya tabbatar da lafiyar wadannan tsuntsaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng