Bayan shekaru 21 a tare, kotu ta raba ma'aurata saboda uwargida ta lashi takobin ba zata sake yiwa miji girki ba

Bayan shekaru 21 a tare, kotu ta raba ma'aurata saboda uwargida ta lashi takobin ba zata sake yiwa miji girki ba

- Saboda daina yiwa miji girki, Alkali ya raba jiha tsakanin mata da miji

- Matar ta bayyana ta daina yiwa mijin girki ne saboda bai yadda da ita ba

- Alkali ya raba yaransu uku kuma ya umurci miji ya rika ba da kudin ciyarwa wata-wata

Wata kotun dake zamanta a Mapo, garin Ibadan a ranar Alhamis ta kwance daurin auren ma'aurata, Ojo Ayeni da matarsa, Shade, bayan sun kwashe shekaru 21 tare.

Kotu ta raba auren ne saboda uwargidar ta kwashe shekaru biyu ba ta yiwa mijinta girki.

Ojo Ayeni ya bayyanawa kuliya cewa rabon da matarsa ta girkawa shi da yaransu uku abinci, tun shekarar 2018.

Yayin yanke hukunci, Alkali mai shari'a, Odunade, ya raba musu jiha don a zauna lafiya.

Ya baiwa mijin babban dansu, yayinda ya baiwa matar sauran yara. Bayan haka an umurci Mijin ya rika biyan matar N10,000 kowani wata don ciyar da yaran.

Bayan shekaru 21 a tare, kotu ta raba ma'aurata saboda uwargida ta lashi takobin ba zata sake yiwa miji girki
Bayan shekaru 21 a tare, kotu ta raba ma'aurata saboda uwargida ta lashi takobin ba zata sake yiwa miji girki
Source: Twitter

DUBA NAN: Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto (Hotuna)

Gabanin yanke hukunci, Ojo Ayeni ya bayyana cewa duk lokacin da ya kai karan matarsa wajen iyayenta, ba ta gyarawa.

"Ya Alkali mai shari'a, kuncin ya tsananta ne lokacin da Sade ta fara yi min isgili duk lokacin da ta gan ni ina yiwa yara girki." Ojo Yace

"Bayan haka, sai cikin dare take dawowa gida kuma hakan ya raba kan mutanen gida."

"Hawan jini ya kama ni sakamakon wannan lamarin kuma ban san daukan doka a hannu na."

A nata jawabin, Shade ta karyata tuhumar da ake mata.

"Hakane, na amince na daina yiwa mijina girki saboda ya zarge ni da kokarin sanya masa guba cikin abinci," Shade tace.

KARANTA NAN: Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel