Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

- Wata mata mai suna Brenda ta auri tsohon mijin 'yar ta mai suna Clive a garin Warrington da ke yankin Cheshire na kasar Ingila bayan ya saki 'yar ta

- Da farko dai hukumomin kasar sun hana su aure domin akwai dokar da ta hana auren surukai amma daga bisani an sauya dokar kuma suka yi aurensu

- Ma'auratan sun ce suna fuskantar tsangwama daga 'yan uwansu har ta kai sun kaurace musu amma hakan bai dame su ba

Wani mutum mai suna Clive Bunden da matarsa Brenda daga Warrington, Cheshire a Ingila sun shafe kimanin shekaru 30 suna zama tare duk da cewa ya taba auren 'yar ta Irene a shekarar 1977.

The Mirror UK ta ruwaito cewa sun fi shekaru 30 suna tare duk da cewa shekarun su 13 da aure duk da irin alakar da ke tsakaninsu.

Da farko hukuma ta kama shi a lokacin da ya nemi surukarsa ta aure shi domin hakan ya saba wa dokar kasar. Sai dai daga bisani sun yi aure bayan an sauya dokar a shekarar 2007.

"Mutane ba su yi tsamanin za mu dade tare ba amma gashi har yanzu kullum sai kara shakuwa muke yi," a cewar Clive mai shekaru 65.

"Muna tare a kowanne lokaci, abin gwanin ban mamaki"

Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa
Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara

Brenda mai shekaru 77 ta kara da cewa, "Clive mutum ne mai dattaku kuma yana kula wa da ni. Wasu lokutan ina son jayayya amma yana shawo kai na."

Brenda ba ta cika son Clive ba a lokacin da ya ke auren 'yar ta Irene.

Hasali ma, a lokacin ba ta son ganin shi.

Irene da Clive sun yi aure a shekarar 1977 kuma sun haifi yara mata guda biyu Sarah da Tanya kafin suka rabu a 1985.

Shekaru hudu bayan rabuwarsu, Clive da Brenda suka fara soyayya a boye.

Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa
Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa
Source: Twitter

A shekarar 1977 suka yi niyyar yin aure. Amma kwanaki kadan bayan sun sanar da ranar aurensu a kotun garinsu na Warrington, Cheshire sai aka kama Clive.

An fada masa cewa akwai wata doka da ta hana mutum ya auri surukarsa kuma za a iya masa daurin shekaru 7 idan ya aure ta.

Saboda mijin Brenda na farko, Richard ya rasu sannan Irene ta sake aure, sun yi tsammanin babu matsala za su iya yin aure.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Katsina za ta bawa tubabbun 'yan bindiga gidaje da shaguna da gonaki

Bayan haka ne Clive ya fara fafutikan ganin an canja wannan dokar da aka kafa shekaru 500 da suka shude.

Sai bayan shekaru 10 sannan wata kotu a Turai ta soke haramcin auren surukai.

"Na tuna lokacin da muka ji labarin a talabijin a Satumban 2005," in ji Clive.

"Nan take na tsuguna na ce Brenda ta aure ni. Idanu na cike da hawaye."

A ranar 17 ga watan Maris na 2007 aka daura musu aure a kotun da Clive ya auri Irene shekaru 30 da suka gabata.

Mafi yawancin iyalansu ba su hallarci daurin auren ba ciki har da Irene. Wani dangin su ne nesa ne kawai ya aiko musu da katin taya murna.

Brenda ta ce 'yan uwan mu ba su cika ziyarar mu ba amma hakan bai dame mu ba domin abinda ke da muhimmanci wurin mu shine kasancewarmu tare.

Clive ya ce hankalinsa ya fi kwanciya bayan an daura musu aure.

A wani labarin, kun ji cewa wani dan kasuwa, Iga Bale, a ranar Laraba ya roki kotun gargajiya da ke Nyanya Abuja ta raba aurensa da matarsa Liza a kan cewa ta rantse sai ta gallaza masa ta mayar da shi tamkar mabaraci.

Bale ya roki wannan alfarman daga hannun kotu ne cikin takardar neman raba aure da ya shigar a kotun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel