Yaro ya fadi matacce bayan ya kwankwadi kwalaben giya 5 yayin gasar shan barasa

Yaro ya fadi matacce bayan ya kwankwadi kwalaben giya 5 yayin gasar shan barasa

- Wani yaro dan makarantar frimare ya yanke jiki ya fadi matacce yayin gasar shan barasa ta yara da aka shirya a Malawi

- Yaron da ba a bayyana sunansa ba ya fadi ya mutu ne bayan da ya shanye kwallaben giya 5 a zagayen karshe na gasar

- Hukumar kiyayye hakkokin yara na kasar ta fara bincike a kan lamarin kuma tana duba yiwuwar haramta shan irin barasar da ta kashe yaron

Wani yaro dan shekara 11 ya mutu bayan ya kwankwadi kwallaben giya a yayin gasar shan barasa na wadanda shekarunsu bai haura 14 ba a Malawi.

Yaron da aka ce dama kwararren mashayi ne ya sha kwalabe biyar na wani barasa mara lasisi mai suna Kachashu da ake yi a gargajiyance.

Yaro ya fadi matacce bayan ya sha kwalaben giya 5 yayin gasar shan barasa
Yaro ya fadi matacce bayan ya sha kwalaben giya 5 yayin gasar shan barasa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara

Ya fadi matacce a yayin da sauran 'yan kallo ke tsaye a wurin gasar a garin Mzimba da ke arewacin Malawi kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Abokan yaron da ba a bayyana sunansa ba sun ce ya yanke jiki ya fadi ne a zagayen karshe na gasar kamar yadda Daily Star ta ruwaito.

An saka kyautar kudi MWK 20,000 (Fam 20.50) ga duk wanda ya lashe gasar.

Jami'in hukumar kare hakokin yara Shanks Nkhata ya ce ya fara bincike a kan lamarin kuma zai yi kokarin tuntubar masu sarautar gargajiya na yankin su hana yin irin wannan barasar da ake yi ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina za ta bawa tubabbun 'yan bindiga gidaje da shaguna da gonaki

Nkhata ya ce: "Mun ji cewa yaron yana aji na bakwai ne a makarantar frimare ta Kafulufulu kuma tunda aka bayar da hutun korona kawai sai ya zama mashayin giya."

A lokacin ganiyar annobar korona, wani mutum ya kusa rasa ransa yayin gasar shan barasa da aka yi ta yanar gizo mai suna ‘Confinement Challenge Apero’ bayan ya sha lita 1.5 na barasa ya suma.

An kwantar da mutumin a asibitin Jami'ar Marie Curie da ke Charleroi a yammacin yankin Belgian ta Hainaut.

A wani labarin kun ji cewa wani dan kasuwa, Iga Bale, a ranar Laraba ya roki kotun gargajiya da ke Nyanya Abuja ta raba aurensa da matarsa Liza a kan cewa ta rantse sai ta gallaza masa ta mayar da shi tamkar mabaraci.

Bale ya roki wannan alfarman daga hannun kotu ne cikin takardar neman raba aure da ya shigar a kotun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel