Yan Boko Haram na cin karnukansu ba babbaka a Arewa maso gabas da yamma kulli yaumin

Yan Boko Haram na cin karnukansu ba babbaka a Arewa maso gabas da yamma kulli yaumin

- Gamayyar kungiyoyin Arewa sun aikawa shugaba Buhari sakon kar ta kwana

- Kakakin kungiyar, AbdulAzeez ya ce duk da ikirarin Soji, ana halaka mutan Arewa

- A ranar Talata yan ta'addan Boko sun kaiwa mutan Borno mumunan hari da yayi ajalin rayuka

Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya ta ce yan ta'adda da yan bindiga na cin karnukansu ba babbaka kulli yaumin a Arewa maso gabas da yammacin Najeriya suna hallaka mutane da dukiyoyi.

A hira da manema labarai a Abuja ranar Laraba, kakakin gamayyar, Abdul-Aziz Suleiman ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen dakile yan bindigan da masu daukan nauyinsu.

Ya ce ya zama wajibi a cire siyasa cikin lamarin samar da tsaro da yaki da yan ta'adda a Arewacin Najeriya.

"Duk da ikirarin da gwamnati da Sojoji keyi cewa sun ci galaba kan yan ta'adda a Arewa maso gabas, mambobin kungiyar basu daina kai hare-hare, kwace barikin Soji, kwace makamai, hallaka mutane ba." Suleiman yace.

KU KARANTA: Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam

Yan Boko Haram na cin karnukansu ba babbaka a Arewa maso gabas da yamma kulli yaumin
CNG/Boko Haram
Asali: Facebook

Legit ta kawo muku labarin cewa yan ta’addan Boko Haram sun sake kai mummunan hari jihar Borno a daren ranar Talata, 15 ga watan Satumba.

Jaridar Sun ta ruwaito cewa harin wanda ya afku a kauyen Wasaram ya yi sanadiyar mutuwar mutum takwas yayinda wasu biyu suka jikkata.

Ali Musa, daya daga cikin mutanen da suka tsere daga kauyen zuwa jihar da ke makwabtaka ta Yobe ya ce yan ta’addan sun kai kimanin su 30.

“Sun zo Wasaram da misalin karfe 8:00 na dare a ababen hawa. Sun kai kimanin su 30. Sai suka fara harbin mutane daga mashigin kauye. Mutane takwas aka kashe sannan aka raunana biyu a harin,” Musa ya bayyana.

Da farko, Legit.ng ta ruwaito cewa kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkareem Lawan, a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba, ya ce akalla kananan hukumomi uku na jihar sun zama fayau sakamakon hare-haren yan ta’adda.

Kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da - Guzamala, Marte da Abadam, duk a yankin arewacin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel