‘Yan kwadago za su yi ta, ta kare da Gwamnati a kan karin kudin fetur, wuta

‘Yan kwadago za su yi ta, ta kare da Gwamnati a kan karin kudin fetur, wuta

- Karin kudin fetur da lantarki ya jawowa Gwamnatin Tarayya fushin Ma’aikata

- Kungiyar kwadago, NLC ta ce Ma’aikata za su tafi yajin-aiki karshen Satumba

- Bayan haka, NLC ta na shirya gudanar da zanga-zanga a fadin jihohin kasar nan

A ranar Laraba, 16 ga watan Satumba, 2020, kungiyar ‘yan kwadago a Najeriya ta NLC ta ba gwamnati wa’adin janye karin da ta yi a kan kudin mai da wuta.

NLC ta ce za ta tafi yajin aiki muddin aka shafe makonni biyu daga yanzu ba tare da gwamnatin tarayya ta maida farashin man fetur da wuta kamar yadda su ke ba.

Kungiyar kwadagon ta ce takwarorinta za su jawo abubuwa su tsaya cak, idan wa’adin da su ka bada ya wuce ba tare da gwamnatin kasar ta lashe aman da ta yi ba.

Shugaban kungiyar NLC, Kwamred Ayuba Wabba, ya shaidawa ‘yan jarida cewa bayan yajin aiki, su na shirya gudanar da gagarumar zanga-zanga a fadin Najeriya.

KU KARANTA: An yi wa Attajirai karin kudin wutar lantarki

Jaridar Daily Trust ta ce wa’adin da kungiyar ta sa shi ne ranar 28 ga watan Satumban nan.

Ayuba Wabba ya karantowa manema labarai matsayar da su ka cinma bayan wani dogon taro na sa’o’i da su ka yi a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba.

Ga abin da jagoran ‘yan kwadagon ya fada: “An gudanar da wannan taro ne domin a duba lamuran karin kudin shan wutar lantarki da farashin man fetur.”

"Babbar majalisa ta CWC ta lura cewa wannan kari da aka yi bai zo a lokacin da ya dace ba, domin kuwa ana fama da annobar COVID-19, da kuma tsadar rayuwa.”

“CWC ta kuma lura cewa wannan tsari ya ragewa ‘yan Najeriya da ma’aikata karfin samunsu.”

KU KARANTA: Majalisa ta yi kokarin hana ayi karin farashin wuta

‘Yan kwadago za su yi ta, ta kare da Gwamnati a kan karin kudin fetur, wuta
NLC ta na barazanar yin yaji
Asali: UGC

“Bayan haka, wannan ya jawo tashin kaya da kudin aiki, bugu da kari, ya cinye ribar da aka samu a karin da aka yi na N30, 000 a matsayin mafi karancin albashi.”

Don haka NLC ta bada wa’adin kwanaki 11 daga ranar Laraba domin a janye wannan kare-kare da aka yi, ko kuma a fuskanci yajin-aiki da zanga-zangar lumuna.

Kwanakin baya kun ji cewa an gudanar da zanga-zanga a jihar Osun, saboda wannan dalili.

Daga baya jami’an tsaro sun rika kama wadanda aka samu su na zanga-zangar lumuna domin nuna rashin jin dadinsu game da yadda aka tada farashin shan wuta da mai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel