Arangama tsakanin magoya baya: Rayuwata ake nema - dan takarar PDP a Ondo

Arangama tsakanin magoya baya: Rayuwata ake nema - dan takarar PDP a Ondo

> INEC ta tsayar da 10 ga watan Oktoba a matsayin ranar gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo

> Tuni 'yan takarar da za su wakilci jam'iyyunsu sun dukufa wajen yawon yakin neman zabe a lungu da sakon jihar

> Dan takarar jam'iyyar PDP, Eyitayo Jegede, ya yi taro da manema labarai bayan wata mummunar arangama tsakanin magoya bayansa da na jam'iyyar APC a Akoko

An yi wata arangama a tsakanin magoya bayan dan takarar jam'iyyar PDP, Eyitayo Jegede, da wasu magoya bayan jam'iyyar APC a garin Oba Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta kudu ma so yamma a jihar Ondo.

Bayan aragamar ne Jegede ya yi korafin cewa an tayar da hargitsin ne tun farko saboda ana neman rayuwarsa.

Jegede ya bayyana cewa an lalata motoci 15 daga cikin motocin da ke cikin tawagarsa tare da raunata wasu daga cikin magoya bayansa.

Ya bayyana cewa an yi hakan ne domin kassara yakin neman zabensa.

Da ya ke magana yayin taro da manema labarai, Jegede ya ce wannan shine karo na biyu da hakan ta taba faruwa, wanda kuma manuniyace kan cewa akwai sa hannun wasu jagororin jam'iyyar APC.

Arangama tsakanin magoya baya: Rayuwata ake nema - dan takarar PDP a Ondo
Eyitayo Jegede
Asali: Twitter

Jegede ya bayyana cewa hatta gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya nuna damuwarsa a kan arangamar yayin tattaunawarsu ta wayar tarho a kan faruwar lamari.

Dan takarar na PDP ya ce sai da ya samu izini daga wurin jami'an tsaro sannan ya shiga karamar hukumar Akoko domin gudanar da yakin zabe, a saboda haka bai kamata a samu wata jam'iyya ta na wani taro ba a yankin.

DUBA WANNAN: Kamfen: Atiku ya mayar da martani bayan Tinubu ya wallafa sakon bidiyo a kan zaben Edo

DUBA WANNAN: Nan da 2022 hawa mota mai amfani da fetur zai fi karfin talaka - FG

"An lalata ma na motoci 15. Da kaina na sanar da kwamishinan 'yan sanda. Wannan magana ce da ta shafi barazana a kan rayuwata," a cewar Jegede.

Jegede ya bayyana cewa ya kira gwamna Akeredolu ne domin sanar da shi yadda magoya bayan jam'iyyar APC su ke kokarin ba ta siyasa ta hanyar kai wa tawagarsa hari yayin da su ka fita yakin neman zabe.

A cewarsa; "za mu yi nasara a wannan zaben, burinsu shine su saka tsoro a cikin zukatanmu don mu gaza fita yakin neman zabe, shi ya sa su ke amfani da bindigu wajen kai wa tawagarmu hari.

"Na sanar da gwamna Akeredolu cewa akwai bukatar mu zauna domin kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kuma tsawatarwa magoya bayanmu da jaddada bukatar samun zaman lafiya har bayan zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng