Hotunan motocin alfarmar da biloniya Otedola ya siya wa 'ya'yansa

Hotunan motocin alfarmar da biloniya Otedola ya siya wa 'ya'yansa

- Babu shakka fitaccen dan kasuwar Najeriya kuma hamshakin mai dukiyar Femi Otedola uba ne nagari

- A cikin kwanakin nan ne aka ga yadda 'ya'yan babban hamshakin mai arzikin suka fantama a dukiyarsa

- Mashahurin mai kudin ya gwangwaje 'ya'yansa mata uku da motocin alfarma kirar Ferrari Portofino kowaccensu

Fitaccen hamshakin mai kudi a Najeriya, Femi Otedola, ya bayyana yanayin kaunar da yake yi wa 'ya'yansa mata uku.

Biloniyan babu shakka uba ne mai kaunar 'ya'yansa domin kuwa cikin kwanakin nan ya fitar da 'ya'yansa siyayya inda ya kashe musu miliyoyin kudi domin siyan motoci.

Otedola ya siya wa kowacce diyarsa mota kirar Ferrari Portofino. 'Ya'yansa da ya siya wa motocin sune Temi, Tolani da DJ Cuppy.

Ya siya musu motar sabuwar fitowa ta shekarar 2020 wacce ake cewa tana da tsananin gudu. Ana siyar da kowacce daya a kan kudi N82.2 miliyan.

Motocin sun zo a launikan da kowacce diyarsa ta fi so. Ta DJ Cuppy ta zo a launin hoda, ta Temi ta zo a launin ruwan kasa sai ta Tolani da ta zo a launin bula.

Cike da annashuwa da farin ciki 'yan matan suka garzaya kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, inda suka wallafa hotunansu tare da sakon godiya ga mahaifinsu.

Katafaren gidan mawakiya Rihanna da ke birnin London wanda ta kwashe kusan shekaru biyu da rabi ana gina shi an daga shi domin siyarwa, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Za a siyar da katafaren gidan a kan pam miliyan 32 wanda yayi daida da Naira biliyan 14, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Gidan mai dakin kwana takwas yana nan a St Johns, yana da kofofi biyar manya tare dakin wanka mai kamar wurin gyaran jiki tare da katafaren lambu.

Katafaren gidan da ke birnin London na da wurin adana motoci har 10, wurin motsa jiki da manyan dakunan nishadi biyu tare da madafi katafare.

An fara gina gidan a 1844 wanda ya zama mallakin Daniel Francis, babban dan kasuwar lu'u-lu'u. Fitaccen magini William Holme Twentyman ne ya gina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel