Yakin neman zabe: Atiku ya mayar wa Tinubu martani a kan zaben Edo

Yakin neman zabe: Atiku ya mayar wa Tinubu martani a kan zaben Edo

- Jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya roki mutanen jihar Edo su juyawa gwamna Godwin Obaseki baya a zaben da za a yi ranar Asabar

- Obaseki ya sanar da Tinubu cewa ba zai iya juya jihar Edo kamar yadda ya ke juya sauran jihohin yankin kudu ma so yamma ba

- A ranar Asabar 19 ga wata hukumar zabe ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben kujerar gwamnan jihar Edo

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci ma su kada kuri'a a jihar Edo su zabi dan takarar jam'iyyar PDP kuma gwamna mai ci, Godwin Obaseki, a zaben ranar Asabar.

Ya saki wannan sakone a shafinsa na tuwita jim kadan bayan jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya fitar da wani sakon faifan bidiyo.

A cikin faifan bidiyon, Tinubu ya roki mutanen jihar Edo su juyawa Obaseki baya ta hanyar zaben jam'iyyar APC a zaben da za a rayi ranar 19 ga wata.

"Obaseki bai cancanci samun kuri'a ba a zabe mai zuwa, kar ku zabeshi, wannan ita ce bukatata a wurinku," a cewar Tinubu.

Sai dai, Obaseki ya mayarwa da Tinubu martani ta hanyar sanar da shi ba zai juya jihar Edo ba kamar sauran jihohin kudu maso yamma.

A cikin nasa martanin, Atiku ya yi gargadin amfani da tashin hankali yayin zaben.

"Mun sha wahala wajen kafa wannan dimokradiyya da mu ke tutiya da ita. Ya kamata mu ke tunanin kara karfafa dimokradiyya ta hanyar yi wa dokoki garambawul.

"Ina bukatar ma su zabe su yi aiki da hankalinsu ta hanyar yin abinda ya dace, watau su yi turuwar fita wajen kada kuri'unsu ga gwamna Obaseki," a cewar Atiku.

Yakin neman zabe: Atiku ya mayar wa Tinubu martani a kan zaben Edo
Atiku da Tinubu
Source: UGC

A jiya, Talata, ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa dan takarar jam'iyyar APC a zaben kujerar gwamnan jihar Ondo kuma gwamna mai ci, Rotimi Akeredolu, ya samu nasara a kan sauran abokan takararsa a zaben gwajin da aka gudanar.

Dan takarar jam'iyyar ZLP kuma tsohon mataimakin Akeredolu, Agboola Ajayi, ne ya zo na biyu yayin da dan takarar jam'iyyar PDP, Eyitayo Jegede, ya zo na uku.

KARANTA: A karshe: Buhari ya fadi dalilin gwamnatinsa na yawan ciyo bashi

KARANTA: An kori lauyoyin Magu yayin zaman kwamitin bincike a fadar shugaban kasa

Kungiyar Coalition ce ta shirya zaben gwajin gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba.

Coalition kungiya ce da ta kunshi jam'iyyun siyasa fiye da 26, kabilu daban-daban, kungiyoyin matasa, mata da sauransu.

Sai dai, an dan samu yamutsi a wurin da aka tattara sakamako domin sanarwa.

Wasu daga cikin wakilan jam'iyyu sun hargitsa wurin ta hanyar yunkurin lalata akwatin kuri'u yayin da ake kidaya kafin sanar da sakamako na karshe.

Sun yi hakan ne domin dakatar da sanar da sakamakon zaben gwaji bayan sun tabbatar da cewa jam'iyyar APC ce za ta lashe zaben.

Sai dai, jami'an tsaro sun gaggauta fitar da wakilan da su ka yi yunkurin kawo hargitsin kuma komai ya koma daidai bayan dan lokaci.

Akeredolu ya samu kuri'u 162 a zaben gwajin da wakilai 400 suka kada kuri'a.

Agboola ya zo na biyu da yawan kuri'u 89 yayin da Jegede ya samu kuri'u 67, sai kuma dan takarar ADC, Prince Adelegan, wanda ya samu kuri'u 6 kacal.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel