Kano: Mutane uku sun mutu sakamakon rushewar wani a gini a Dawanau

Kano: Mutane uku sun mutu sakamakon rushewar wani a gini a Dawanau

- Wani gini ya rushe a unguwar Dawanau, karamar hukumar Dawakin Tofa, sakamakon mamakon ruwan sama

- A ranar Talata ma wani ginin bene ya rushe a unguwar Gwammaja 'Yan Kosai da ke yankin karamar hukumar Dala a jihar Kano

- Mutane uku ne aka tabbatar da cewa sun rasa ransu yayin da wasu mutanen 8 su ka samu munanan raunku

Mutane uku ne su a rasa rayukansu yayin da wani gini ya rushe a garin Dawanau a karamar hukumar hukumar Dawakin Tofa, jihar Kano.

A cewar jaridar Punch, ginin ya rushe ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a daraen ranar Talata a Kano.

Mallam Buba Anwar, mahaifin daya daga cikin wadanda su ka rasu, ya ce ginin ya rushe ne da mialin karfe 03:00 na safiya yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren ranar Talata.

A cewar Anwar, ya ji a jikinsa cewa ginin zai iya rushewa, a saboda haka sai ya umarci matarsa ta kwashe yaransu daga dakinsu.

Sai dai, a yayin da iyayen su ka samu nasarar tserar da yarinyarsu, sun rasa yarasnu namiji sakamakon rushewar ginin.

A wani labarin mai kama da wannan, wani bene ya rushe a sa'o'in farko na ranar Talata inda aka rasa rayukan mutum biyu kuma 'yan gida daya a unguwar Gwammaja 'Yan kosai da ke karamar hukumar Dala.

An gano cewa, mutum takwas duk a gida dayan sun samu manyan raunuka bayan sun kasa fitowa daga ginin da ya fadi.

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano, Sa'adu Muhammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Vanguard.

Ya ce Abdullahi Anas da Abdulmalik Anas sun riga mu gidan gaskiya.

Kano: Mutane uku sun mutu sakamako rushewar wani a gini a Dawanau
Rushewar gini
Source: Original

Muhammed ya ce, "Mun samu kiran gaggawa daga wani Malam Abdullahi Muhammad daga Gwammaja 'yan Kosai a karamar hukumar Dala ta jihar Kano.

"Ya kira wurin karfe 1:30 na dare inda ya tabbatar da cewa wani gidan bene ya fadi."

"Bayan samun kira, mun gaggauta isa da kayan aiki wurin inda muka tara da iyalan a cikin mugun hali.

"An mika dukkan wadanda ginin ya fada musu asibitin Murtala Muhammad inda aka tabbatar da mutum biyu sun rasu," a cewarsa.

KARANTA: Ku godewa Allah: Kamata ya yi a sayar da litar man fetur N181 ba N161 ba - FG

KARANTA: Zaben 2020: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda bai cika ba a Amurka

A wani labari na daban, masu taimako daga kasar Indiya sun tono wani yaro dan shekara hudu da rai daga cikin burbushin gini da ya danne shi tsawon kwana daya yana karkashi.

Mutane sunyi ta murna a ranar Talata 25 ga watan Agusta, bayan an tono yaron daga karkashin ginin da ya danne shi mai hawa biyar.

Bayan yaron, ginin kuma ya danne mutum 70 a wajen.

Lamarin dai ya faru a ranar Litinin 24 ga watan Agusta, a yammacin garin Mahad, dake kudancin Mumbai.

Sai da aka sanya ma'aikata da yawan gaske da kuma karnuka masu jiyo kamshin abu, inda suka yi ta aiki har zuwa cikin dare suna dauke da bulo da kwanika duka wajen neman wadanda ke da kwana a gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel