Matata ta rantse sai ta gallaza wa rayuwa ta, ta talauta ni: Miji ya fada wa kotu

Matata ta rantse sai ta gallaza wa rayuwa ta, ta talauta ni: Miji ya fada wa kotu

- Wani magidanci a garin Abuja ya yi karar matarsa a kotu inda ya ke nema a raba aurensu

- Mutumin ya yi ikirarin cewa matarsa tana boye abinci a gidansa da niyyar ganin sai ta talauta shi kaman mabaraci

- Ya kuma yi ikirarin cewa matar tana soyayya da wani a waje duk da cewa duk ta musanta zargin da mijin ya yi

Wani dan kasuwa, Iga Bale, a ranar Laraba ya roki kotun gargajiya da ke Nyanya Abuja ta raba aurensa da matarsa Liza a kan cewa ta rantse sai ta gallaza masa ta mayar da shi tamkar mabaraci.

Bale ya roki wannan alfarman daga hannun kotu ne cikin takardar neman raba aure da ya shigar a kotun.

Matata ta rantse sai ta gallaza wa rayuwa ta, ta talauta ni: Miji ya fada wa kotu
Matata ta rantse sai ta gallaza wa rayuwa ta, ta talauta ni: Miji ya fada wa kotu. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da ɗansa a Katsina

"Da jarin kasuwanci ne ya karya, na koma Abuja da zama. Na samu aiki da wani kamfani mai zaman kansa na kuma dako matata da yara na su dawo Abuja tare da ni.

"Da matata ta zo, na ce tayi maneji da karamin aikin da na samu har zuwa lokacin da babban aiki sai samu.

"Duk da cewa ta yarda, bayan kankanin lokaci sai ta fara boye abincin da ta ke siya da kudin da na ke bata.

"Tana barnatar da abinci domin dai a rasa abinda za a ci a gidan.

"Da na yi mata magana a kan hakan, sai ta ce niyyar ta shine ta kashe dukkan kudi na har sai na talauce kamar mabaraci.

"Ta zubar da cikin da ta dauka bayan watanni hudu, likitan da ya zubar mata ma soyayya su ke yi,' kamar yadda mijin ya yi ikirari.

KU KARANTA: Cacar baki a kan siyan shawarma ya yi sanadin mutuwar wani mutum a Legas

Wacce aka yi karar ta, Liza ta musanta dukkan zargin da mijin ta ya yi.

Alkalin kotun, Shitta Muhammad ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 22 ga watan Oktoba domin wacce aka yi karar ta kare kanta.

A wani labarin daban, kun ji cewa wata mata mai sana'ar treda, Fisayo Akibu a ranar Talata ta tafi kotun gargajiya da ke zamansa a Mapo Ibadan tana neman a raba aurenta da mijinta Abiodun saboda yawan yin caca da ya ke yi.

A yayin da ta ke magana gaban alkali, matar mai yara hudu ta ce: "Miji na yana yin caca da dukkan kudin da ya ke samu a maimakon kula da ni da yara na.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel