'Yan daba sun kai wa tawagar Gwamnan APC hari, sun ragargaza ababen hawa

'Yan daba sun kai wa tawagar Gwamnan APC hari, sun ragargaza ababen hawa

- Kusan kwanaki 23 suka rage zaben gwamna a jihar Ondo, 'yan daba sun kai wa 'yan takarar PDP da na APC mummunan hari

- Kamar yadda dukkan 'yan takarar suka sanar, sun zargi abokan hamayyarsu da kai musu hari tare da kone motocin kamfen

- Kamar yadda mai magana da yawun Gwamna Akeredolu ya sanar, ya ce wannan harin abun takaici ne kuma babu shakka PDP ce ta kitsa

Kasa da kwanaki 23 da suka rage na zaben gwamna a jihar Ondo, 'yan daban siyasa sun kai wa tawagar Gwamna Rotimi Akeredolu da dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP, Eyitayo hari.

Dukkan 'yan takarar sun isa karamar hukumar Akoko ta kudu maso yamma, domin yakin neman zaben da za a yi a ranar 10 ga watan Oktoba a jihar.

Dukkan masu bai wa 'yan takarar shawara ta musamman, sun zargi abokan adawarsu da wannan harin a takardar da suka fitar a Akure.

Yayin da gwamna Akeeredolu ya zargi magoya bayan Jegede da kai masa hari, hakazalika Jegede ya zargi 'yan daban Akeredolu da kai masa hari.

Mai magana da yawun kungiyar kamfen ta Akeredolu, Richard Olabode, ya zargi 'yan daban PDP da kaiwa gwamnan hari a Oba-Akoko tare da banka wa motar kamfen wuta.

Amma kuma, Jegede Eyitayo, dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP, ya zargi 'yan daban Akeredolu da kai masa hari da kuma kone masa ababen hawa goma.

KU KARANTA: Katsina: 'Yan bindiga sun kashe Sarkin Tauri da wani mutum 1, sun sace mutane masu yawa

'Yan daba sun kai wa tawagar Gwamnan APC hari, sun ragargaza ababen hawa
'Yan daba sun kai wa tawagar Gwamnan APC hari, sun ragargaza ababen hawa. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon tambari (Hotuna da Bidiyo)

A wani labari na daban, dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da tawagarsa ta kamfen a ranar Laraba an kai musu hari.

Wasu bata gari ne ko 'yan daba suka tare su a gunduma ta gona da ke Uzairue, karamar hukumar Etsako.

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole dan asalin yankin ne. Gwamnan tare da magoya bayansa sun kama hanyar zuwa gunduma ta 10, Apana, Uzairue, a lokacin da 'yan daba suka kutsa cikin tawagar kamfen din su.

Sun hari 'yan kauyen tare da wasu magoya bayansa da suka hadu don karbar bakuncin gwamnan da tawagarsa.

Shigar jami'an tsaro lamarin ne yasa 'yan daban suka tsere bayan musayar ruwan wutar da aka yi da su na minti biyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel