Buhari ya sanar da dalilin hana shigo da kayan abinci kasar nan

Buhari ya sanar da dalilin hana shigo da kayan abinci kasar nan

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da dalilinsa na hana shigo da kayan abinci cikin kasar nan

- Ya ce samar da aikin yi tare da fatattakar zaman kashe wando tare da inganta aikin noma ne babban dalilin

- Shugaban yace babu shakka da Najeriya bata dauka wannan matakin ba, da tuni ta fada cikin babbar matsala

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya ce gwamnatin tarayya ta hana shigo da kayan abinci ne domin ta bunkasa aikin noma tare da tseratar da 'yan Najeriya daga rashin aikin yi.

Ya jaddada cewa, noma babbar hanya ce ta samar da ababen bukata, rage zaman kashe wando da fatattakar talauci daga kasar nan, Channels TV ta wallafa.

"Domin ganin mun dawo da samar da kayan bukata, dole ne marasa aikin yi ballantana wadanda basu yi karatu ba su fada harkar noma.

"Da ace bamu koma gona ba, da yanzu muna cikin matsala. Hakan ne yasa dole aka haramta shigo da kayayyakin abinci domin samar da aiki," shugaban kasa yace.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wani taro da yayi ta yanar gizo da kwamitin bada shawara a kan tattalin arziki a gidan gwamnati da ke Abuja.

Shugaban kasar ya kara da bayyana dalilinsa na karbo bashi domin samar da ababen more rayuwa. Ya ce gwamnatinsa tana cin bashin ne domin 'yan kasar.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuka 8, gonaki sun kwashe a Katsina

Buhari ya sanar da dalilin hana shigo da kayan abinci kasar nan
Buhari ya sanar da dalilin hana shigo da kayan abinci kasar nan. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kada ku karya tattalin arzikin Najeriya da korona - Majalisar dattawa

"Muna da kalubale masu tarin yawa da ababen more rayuwa. Dole ne mu karbo bashi saboda tituna, titunan jirgi da kuma wutar lantarki. Hakan zai janyo ra'ayin masu zuba hannayen jari," shugaban kasar ya kara da cewa.

Ya jajanta yadda rashin samar da ababen more rayuwa ballantana a fannin sufuri ya hana kasar nan kaiwa inda ya kamata a fannin sufurin kayayyaki ta jiragen sama da na ruwa a yankin arewa ta yamma.

A wani labari na daban, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana wasu babban dalilan da ya sa gwamnatinsa take ciyo bashi.

A cewar shugaba Buhari, gwamnatinsa ta na ranto kudade ne domin gudanar da aiyukan raya kasa da zasu jawo hankalin ma su zuba jari a tattalin arziki.

A wani jawabi da kakakin shugaba Buhari, Garba Shehu, ya fitar, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yi wannan bayani ne yayin wani taro da mambobin kwamitin bayar da shawara kan tattalin arziki (PEAC). Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel