'Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da ɗansa a Katsina

'Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da ɗansa a Katsina

- Yan bindiga sun kai hari gidan wani ɗan kasuwa, Alhaji Usman Mai Yadi sun kashe shi a daren ranar Litinin

- Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da ɗansa mai suna Usman bayan kashe mahaifinsa a garin Yankara da ke Katsina

- Yayan Usman mai suna Younusa Mukhtar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya yi addu'ar Allah ya jikan mahaifinsa ya kuma kubutar da kaninsa

Wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun kashe wani Alhaji Mai Yadi sun kuma sace ɗansa, Usman a garin Ƴankara da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin, Kwamared Younusa Mukhtar ya tabbatar da afkuwar hakan a ranar Talata 15 ga watan Satumba ya ce lamarin ya faru misalin ƙarfe 11 na daren ranar Litinin a gidansu.

Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da dansa a Katsina
Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da dansa a Katsina
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Cacar baki a kan siyan shawarma ya yi sanadin mutuwar wani mutum a Legas

"Ta faru ta kare: Ɓarayi sun kashe mahaifi na Alhaji Muntari Mai Yadi sannan sun yi garkuwa da ƙani na Usman," kamar yadda ya rubuta.

"Daga Allah mu ke kuma gare shi za mu koma, ɓarayi sun zo gidan mu sun kashe mahaifi na sun tafi da ɗan uwana kuma sun 'amsa waya ta da babur'.

"Sannan ni kai na da kyar na sha bayan duka na da kan bakin bindiga da kyar na sha bayan na ruga da gudu sauran abubuwan bansan yadda suka faru ba.

"Karfe 11:00pm suka shigo babu wani dauki da wani soja ko wani ya kawo mana hakan ya nuna sojojin da aka kawo a Faskari basu da amfani Allah ya isa bamu yafe ba wannan tsinanniyyar gwamnati ce, Allah ya gafartama mahaifina," kamar yadda Yousofu ya rubuta.

KU KARANTA: Mutum 5 sun mutu, takwas sun jikkata sakamakon hatsarin mota a hanyar Ondo

An yi wa wanda ya rasu jana'iza a ranar Talata bisa koyarwar addinin musulunci a gidansa.

Kazalika, a daren ranar Lahadi, wasu ƴan bindigan da ba a san ko su wanene ba sun sace mata huɗu ciki har da ƙaramin yaro a lokacin da suka kai hari Ƴankara.

Garin Ƴankara yana kan iyakan Katsina da Zamfara ne.

A wani labarin daban, kun ji 'yan bindiga sun sace jami'in hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, tare da dansa mai shekaru hudu a ranar Asabar a jihar Kaduna.

Jami'in da a yanzu ba a bayyana sunansa ba ya fada hannun masu garkuwar ne a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a ranar Litinin kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel