Zargin majalisar tarayya kan badaƙalar NDDC - Akpabio ya yi amai ya lashe

Zargin majalisar tarayya kan badaƙalar NDDC - Akpabio ya yi amai ya lashe

- Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta, ya yi amai ya lashe kan ikirarinsa na cewa yan majalisa ne suka samu babban kaso a kwangilolin NDDC

- Akpabio ya ce sam shi bai yi wannan zargin ba a kan yan majalisar

- Ya bayyana jajircewarsa wajen ganin burin Buhari ya cika na samun kyakyawar alaka tsakanin bangaren dokoki da na zartarwa

Ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya ce shi bai zargi yan majalisar dokokin tarayya da amfana daga kwangilolin hukumar kula da ci gaban Neja Delta ba.

Amma hakan ya fito ne daga wani ikirari da ya yi a watan Yuli, jaridar The Cable ta ruwaito.

Yayinda ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai da ke binciken zargin da ake yiwa hukumar da badakalar naira biliyan 815, ministan ya ce "mambobin majalisar dokokin kasar ne suka samu babban kaso na kwangilolin da hukumar ta bayar."

Kan haka, sai Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilan ya bukace shi da ya ambaci sunayen yan majalisar ko kuma ya hadu da fushin majalisar.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: PDP ta jinjinawa Buhari kan wani ƙoƙari da ya yi

Zargin majalisar tarayya kan badaƙalar NDDC - Akpabio ya yi amai ya lashe
Zargin majalisar tarayya kan badaƙalar NDDC - Akpabio ya yi amai ya lashe Hoto: Akwa Ibom Online
Asali: Twitter

Tsohon Shugaban marasa rinjayen ya ambaci sunayen Peter Nwaoboshi, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan NDDC, Matthew Urhoghide, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan asusun gwamnati.

Sai kuma James Manager, sanata mai wakiltan Delta ta kudu, a matsayin wasu daga cikin wadanda suka amfana. Dukkaninsu sun karyata aikata wani abu da ya saba doka.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Olatunji Ojo, mukaddashin magatakardar majalisar dokoki, Akpabio ya ce kawai dai Gbajabiamila ya so sanin ko akwai ‘ba daidai ba’ daga yan majalisar dokokin tarayya.

“A’a, kun yi kuskure. Ba abunda kakakin majalisa ya nema ba kenan,” in ji ministan yayinda yake amsa tambayoyi daga yan jarida.

“Kakakin majalisar ya so sanin ko akwai rashin bin ka’ida daga kowani bangare na majalisar dokoki ta bangaren kwangilolin NDDC. Bai yi magana kan ko sune yan kwangila ba, don haka yanzu nake jin haka daga gareku.”

Akpabio ya ce zai koma majalisar dokoki da zaran yan majalisar sun dawo daga hutunsu.

KU KARANTA KUMA: Kada ku karya tattalin arzikin Najeriya da korona - Majalisar dattawa

“Wannan tamkar dawowa gida ne kuma ya kamata majalisar dokokin ta dawo a yau (Talata). Sun dage dawowar, don haka naso ace da zaran an dawo, gani nan.

“Yana daga cikin kokarina na tallafa shawarar Shugaban kasa cewa dole a samu alaka mai kyau tsakanin bangaren zartarwa da na dokoki."

Tsohon shugaban na marasa rinjaye a majalisa ya ce gwamnati na so ta bar manufa ga ‘yan Najeriya inda ya kara da cewa “ba za mu iya yin haka ba idan babu hadin kai tsakanin dukkanin bangararorin gwamnati.”

A gefe guda, majalisar dattawa a ranar Talata, 1 ga watan Satumba, ta bayyana cewa mambobinta basu karbi naira miliyan 20 na tallafin korona daga NDDC ba.

Daraktan ayyuka na kwamitin rikon kwarya na NDDC, Dr Cairo Ojougboh, ya yi zargi a hira da ya yi da wata jarida a kwanan nan cewa hukumar ta bai wa ýan majalisa kudi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel