Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Biu

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Biu

- Shugaban Najeria, Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga gwamnati, iyalai da al'ummar Borno bisa rasuwar Sarkin Biu, Alh. Mai Aliyu

- Shugaba Buhari ya aike da sakon ta'azziyar ne cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren watsa labarai, Femi Adesina ya fitar

- Shugaban kasar ya yi waiwaye a kan irin halaye masu kyau na marigayin Sarkin ya kuma yi addu'ar Allah ya gafarta masa ya bawa al'umma hakurin jure rashinsa

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya yi alhinin rasuwar Sarkin Biu, Alhaji Mai Aliyu da ya rasu a ranar Litinin 14 ga watan Satumban 2020.

Sakon shugaban kasar na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar mai taken "Shugaba Buhari yana yi wa gwamnatin jihar Borno ta'aziyya game da rasuwar Sarkin Biu."

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Biu
Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Biu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi

Sanarwar ta ce, "Shugaba Muhammadu Buhari yana mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnati da al'ummar jihar Borno bisa rasuwar Sarkin Biu, Alhaji Mustapha Umar Aliyu.

"Shugaban kasar kuma yana taya iyalan sarkin da daukakin masarautar Biu bakin ciki bisa rasuwar Mai martaba wanda ya shafe shekaru 31 yana yi wa mutanensa jagoranci bisa gaskiya da sadaukar da kai.

"Buhari ya jadada cewa Sarkin mutum ne mai kaunar zaman lafiya da cigaba a yankin Arewa maso Gabas kuma mutum ne mai hangen nesa da kowa zai iya gani musamman saboda goyon bayan da ya bayar na zamanantar da Biu ta hanyar kafa makarantu.

KU KARANTA: Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

"Shugaban kasar ya ce irin shugabancin Sarkin na yi wa al'umma hidima ya sa mutanensa sun amince da shi kuma ya samu karamci a idon 'yan Najeriya daga 'yan siyasa da malaman addini.

"Ya yi imanin cewa za a cigaba da tunawa da sarkin saboda ayyukan alherin da ya yi a yankin Arewa ta Gabas, inda ya yi addu'ar Allah ya jikan sarkin ya kuma bawa al'ummar biyu hakurin jure rashinsa."

A wani labarin, kun ji cewa mashawarcin Gwamnan Benue, Samuel Ortom a kan harkokin Kananan hukumomi da masarautu, Hon. Jerome Torshimbe ya rasu.

Toshimba ya rasu a yammacin ranar Litinin a wani asibiti da ke Abuja. Ya rasu yana da shekaru 63 a duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel