Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya

Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya

- Fitaccen marubuci kuma wanda ya karba kyautuka da dama, Farfesa Wole Soyinka, ya kalubalanci shugaba Buhari

- Farfesan ya jaddada cewa dole ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka matakin gaggawa a kan salon mulkinsa

- Ya ce babu shakka akwai yuwuwar dukkanmu mu fada halaka matukar aka cigaba da tafiya a yadda ake

Fitaccen marubuci Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauya salon mulkin Najeriya, ko kuma akwai yuwuwar dukkanmu za mun fada halaka.

Ya tabbatar da cewa, salon Najeriya babu shakka ba zai haifar da da mai ido ba.

Soyinka wanda ya sanar da hakan a wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar Talata, ya ja kunne a kan rabe-raben kan da ake samu a kasar nan wanda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi magana a kai.

DUBA WANNAN: A wurin caca miji na ya ke kashe dukkan kudinsa: Mata ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta

Ya jaddada cewa, babu gwamnatin da za a zuba wa ido ba tare da kalubale ba. An zabeta ne domin ta samar da cigaba. Babu kuwa dalilin da zai sa a kwashe shekaru hudu ana mulki ba tare da an samu wani cigaba ba.

Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya
Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

Soyinka ya yi wannan kirar ne bayan da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi gargadi mai kama da wannan inda ya ce kawunnan yan kasar ya rabu kuma tana hanyar rugujewa.

Obasanjo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a wurin wani taron da kungiyoyi masu wakiltan yankunan kasar suka hallarta.

KU KARANTA: Cacar baki a kan siyan shawarma ya yi sanadin mutuwar wani mutum a Legas

Taron da aka yi a ranar Alhamis 10 ga watan Satumba a Abuja ya samu hallarci kungiyoyi kamar Afenifere, Middle Belt Forum, Northern Elders Forum, Ohanaeze Ndigbo da sauran su.

Tsohon shugaban kasar ya ce bai taba ganin rabuwar kai a Najeriya ba kamar wadda aka samu a ƙarƙashin gwamnatin Buhari.

Ya kuma nuna bakin cikinsa a kan yadda Najeriya da zama babban birnin talauci na duniya.

"Na ji dadin yadda kuma kuke bakin cikin halin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a yanzu.

A yanzu Najeriya ta kama hanyar rugujewa ga kuma rarrabuwar kai; a fanin tattalin arziki kasar mu kama hanyar zama babban birnin talauci na duniya ga kuma rashin tsaro," kamar yadda Obasanjo ya fadi a wani sashi na jawabinsa.

A wani rahoton daban, kun ji cewa kungiyar dattawan arewa a ranar Lahadi da dare ta bayyana dalilinta na tattaunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo tare da kungiyar Afenifere.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce sun tattauna da su domin shawo kan matsaloli da manyan kalubale da ke addabar kasar nan, Daily Trust ta wallafa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel