UK tana barazanar kwace kadarorin 'yan siyasar da za su yi magudi a zabukan Edo da Ondo

UK tana barazanar kwace kadarorin 'yan siyasar da za su yi magudi a zabukan Edo da Ondo

- Kasar Ingila ta fitar da jan kunne tare da babbar barazana ga duk wadanda ke da tunanin magudin zabe a jihohin Edo da Ondo

- Kamar yadda wata takardar da ofishin jakadancin Ingila ya fitar, ya ce akwai yuwuwar kwace kadarorin duk wanda ta kama

- Ta ce kawancenta da Najeriya ba zai sa ta zuba ido tana ganin ana karantsaye ga damokaradiyya ba

Kasar Ingila tana yin babbar barazana ga duk wanda ta kama da hannu cikin magudin siyasa a zabukan gwamnoni jihohin Ondo da Edo masu gabatowa.

A wata takardar da ta fita a ranar Talata, ofishin jakadancin Ingila da ke Najeriya ya yi barazanar kwace kadarorin kasashen ketare da duk wanda aka kama da laifin.

Sau da yawa, zabukan Najeriya na cike da magudi na kwace akwatunan zabe da kayayyakin zabe, kamar yadda ya faru a jihohin Kogi da Bayelsa.

A wata takardar da aka wallafa ta Twitter, Ingila ta ce za ta tura masu lura da zabuka a dukkan jihohin biyu da za a yi zabe.

"A matsayin kawaye ga Najeriya, za mu bibiyi zabukan jihohin Edo da Ondo, wadanda za a yi a watannin Satumba da Oktoba," tace.

"Wadannan zabuka na da matukar muhimmanci, dukkansu suna da amfani wajen karfafa damokaradiyyar Najeriya.

"Za mu tura masu lura da zabuka a yayin zabukan jihohin Edo da Ondo domin taimakawa kungiyoyi masu zaman kansu da za su lura da zaben.

KU KARANTA: Zulum zai dauki ma'aikatan lafiya 594 a fadin jihar Borno

UK tana barazanar kwace kadarorin 'yan siyasar da za su yi magudi a zabukan Edo da Ondo
UK tana barazanar kwace kadarorin 'yan siyasar da za su yi magudi a zabukan Edo da Ondo. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matar da tace takalmi yafi kanin mijinta daraja tayi dana sani bayan yayi kudi yayi mata goma ta arziki

"Ingila bata maraba da duk wani almundahana ko tarzoma da ta shafa zabe kamar yadda muka yi a zabukan 2019. Za mu cigaba da daukar mataki a kan duk wanda muka ga yana da hannu a lamarin.

"Wannan zai iya hada wa da saka takunkumin hana shiga Ingila, kwace kadarorin mutum da ke kasar da kuma ladabtar da shi da dokokin kasa da kasa.

"Ingila za ta cigaba da samar da goyon baya a yayin da muke tunkarar zabukan. Muna kira ga INEC, 'yan sanda da sauran cibiyoyi da ke da hannu a zabukan da su jajirce wurin tabbatar da an yi zaben gaskiya," ta kara da cewa.

A wani labari na daban, gwamnatin Amurka ta ce ta saka wa wasu mutane takunkumi hana su shigar ƙasar ta saboda magudin zabe da suka yi yayin zabukkan gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa da aka yi a 2019.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake shirin yin zabukkan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo a watan Satumba da Oktoba na 2020. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel