Ka kyale Obaseki, ka fuskanci makiyan siyasa na APC - PDP ga Tinubu

Ka kyale Obaseki, ka fuskanci makiyan siyasa na APC - PDP ga Tinubu

- Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta yi kira da babbar murya ga babban jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu

- Ta shawarci Ahmed Bola Tinubu da ya sakar wa Godwin Obaseki mara yayi fitsari a jihar Edo

- Ta ce ya fara shawo kan manyan makiyan damokaradiyya, faston bogi kuma ba abun amince ba da ke APC

A ranar Talata, jam'iyyar PDP ta shawarci shugaban jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu da ya shafa wa Godwin Obaseki, dan takarar Gwamnan jihar Edo, lafiya.

Ta shawarci Tinubu da ya fuskanci manyan makiyan da ke cikin jam'iyyar APC, Vanguard ta wallafa.

Tinubu ya ja kunnen jama'ar jihar Edo da kada su goyi bayan Obaseki domin bai cancanci a zabesa ba a matsayin shugaba.

A yayin martani ga bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani, PDP ta bakin sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan, ya ce Tinubu ya saba dukkan dokokin damokaradiyya.

Ya yi kokarin nuna isarsa da iyawa ga jama'ar jihar Edo tare da bayyana musu wanda za su zaba ba don cancanta ba.

KU KARANTA: Matar da tace takalmi yafi kanin mijinta daraja tayi dana sani bayan yayi kudi yayi mata goma ta arziki

Ka kyale Obaseki, ka fuskanci makiyan siyasa na APC - PDP ga Tinubu
Ka kyale Obaseki, ka fuskanci makiyan siyasa na APC - PDP ga Tinubu. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon wajen da aka binne marigayi Sanata Ajimobi da aka cika wajen da kayan alatu, da wutar lantarki wacce bata daukewa

Kamar yadda takardar ta bayyana: "Babu shakka abun takaici ne yadda Asiwaju yake kokarin nuna shine shugaban dukkan Najeriya wanda kuma ba hakan bane.

"A yayin da yake take manyan dokokin damokaradiyya, wanda shine barin jama'a su zaba wanda suke so ba tare da an tirsasa su ba.

"Akwai alamun munafurci ga wanda yake ikirarin zama masoyin damokaradiyya amma kuma a lokaci daya yana zaune a gidansa yana zagin jama'ar jihar Edo a kan zabinsu.

"Asiwaju bai kamata ya cigaba da ikirarin zama masoyin damokaradiyya ba, amma yana kushe zabin jama'ar jihar Edo. Ya fara yakar makiyan cikin gida, mai dabi'u marasa kyau, faston bogi wanda bai kamata a amince da shi ba, Adams Oshiomhole."

A wani labari na daban, babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi kira ga al'ummar jihar Edo suyi watsi da gwamna Godwin Obaseki, dake neman zarcewa kan kujerarsa.

A faifan bidiyon da tasahar TVC ta saki, Tinubu ya ce Obaseki ba jarumin demokradiyya bane kuma a yi waje da shi a zaben gwamnan ranar Asabar.

Tinubu na cikin jiga-jigan APC da suka yiwa Obaseki yakin neman zabe a shekarar 2016 karkashin jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel