'Yan bindiga sun sace tsohon sojan Amurka a Ekiti

'Yan bindiga sun sace tsohon sojan Amurka a Ekiti

- 'Yan bindiga sun kai hari wata masana'antar sarrafa manja sun sace wani tsohon sojan Amurka da mutum guda

- Yayin harin da yan bindigan suka kai a masana'antar man ja da ke Ekiti, sun bindige wani ma'aikacin wurin guda daya ya mutu

- Rundunar yan sanda ta Ekiti ta tabbatar da afkuwar lamarin kuma ta aike da jami'anta da ke aiki tare da mafarauta don kamo yan bindigan

An yi garkuwa da wani tsohon sojan Amurka, Manjo Jide Ijadare (mai murabus) da wani mutum guda a masana'antarsa na sarrafa manja da ke Ijan-Ekiti a karamar hukumar Gbonyin da ke jihar Ekiti.

An ruwaito cewa yan bindiga su bakwai ne suka kai farmaki a masana'antar a ranar Talata misalin karfe 2 na rana inda suka harbe wani ma'aikacinsa guda har lahira kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Bidiyo: An tilasta wa ɓarawon kaza cin ɗanyen kazar da aka kama shi ya sata

'Yan bindiga sun sace tsohon sojan Amurka a Ekiti
'Yan bindiga sun sace tsohon sojan Amurka a Ekiti. Hoto daga The Punch
Asali: Facebook

Wasu shedun ganin ido sun ce yan bindigan da suka kai su bakwai sun kai farmaki masana'antar inda suke harbe wani ma'aikaci a kokarinsu na sace tsohon sojan da wani mutum guda.

"Sun shigo masana'antar da bindigu suka fara harbe-harbe. Sun harbe ma'aikaci daya sun kashe shi nan take.

"Daga nan sai suka fita da Manjo Ijadare da wani ma'aikacinsa guda daya suka yi awon gaba da su a cikin mota zuwa wani wurin da babu wanda ya sani," in ji majiyar.

KU KARANTA: Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Majiyar ya ce maharan sun tsere ne ta hanyar Ise Ekiti.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Ekiti, Mista Sunday Abutu ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce an kashe mutum guda yayin harin.

"Mun tabbatar cewa an sace wani tsohon sojan Amurka da wani mutum guda misalin karfe 2 na ranar Talata.

"An kuma kashe mutum guda daya a masana'antar a Ijan Ekiti inda aka sace mutum biyu.

"Kwamishinan yan sandan ya aike da wasu jami'ai zuwa wurin domin bin sahun su cikin dajin da ke hanyar inda suka bi.

"Yan sanda na aiki tare da mafarauta a garin domin tabbatar da cewa an kama masu garkuwa da mutanen kuma sun fuskanci hukunci."

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun sace jami'in hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, tare da dansa mai shekaru hudu a ranar Asabar a jihar Kaduna.

Jami'in da a yanzu ba a bayyana sunansa ba ya fada hannun masu garkuwar ne a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a ranar Litinin kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel