Ondo: Bidiyon yadda zaben gwaji ya haifar da hargitsi yayin da APC ta samu nasara

Ondo: Bidiyon yadda zaben gwaji ya haifar da hargitsi yayin da APC ta samu nasara

> Ranar 10 ga watan Oktoba hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsayar domin gudanar da zaben kujerar gwamnan jihar Ondo

> Wata kungiya mai suna Coaliton ta gudanar da zaben gwaji a tsakanin 'yan takarar jam'iyyun da ke da 'yan takara a zaben

> Shugaban kungiyar Coalition, Akin Akinbobola, ya ce duk wanda ya samu nasara a zaben gwajin shine zai lashe zaben da INEC za ta gudanar

Dan takarar jam'iyyar APC a zaben kujerar gwamnan jihar Ondo kuma gwamna mai ci, Rotimi Akeredolu, ya samu nasara a kan sauran abokan takararsa a zaben gwajin da aka gudanar.

Dan takarar jam'iyyar ZLP kuma tsohon mataimakin Akeredolu, Agboola Ajayi, ne ya zo na biyu yayin da dan takarar jam'iyyar PDP, Eyitayo Jegede, ya zo na uku.

Kungiyar Coalition ce ta shirya zaben gwajin gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba.

Coalition kungiya ce da ta kunshi jam'iyyun siyasa fiye da 26, kabilu daban-daban, kungiyoyin matasa, mata da sauransu.

Sai dai, an dan samu yamutsi a wurin da aka tattara sakamako domin sanarwa.

Ondo: Bidiyon yadda zaben gwaji ya haifar da hargitsi yayin da APC ta samu nasara
Jegede da Akeredolu
Source: Instagram

Wasu daga cikin wakilan jam'iyyu sun hargitsa wurin ta hanyar yunkurin lalata akwatin kuri'u yayin da ake kidaya kafin sanar da sakamako na karshe.

Sun yi hakan ne domin dakatar da sanar da sakamakon zaben gwaji bayan sun tabbatar da cewa jam'iyyar APC ce za ta lashe zaben.

Kalli faifan bidiyo a nan:

Sai dai, jami'an tsaro sun gaggauta fitar da wakilan da su ka yi yunkurin kawo hargitsin kuma komai ya koma daidai bayan dan lokaci.

Akeredolu ya samu kuri'u 162 a zaben gwajin da wakilai 400 suka kada kuri'a.

Agboola ya zo na biyu da yawan kuri'u 89 yayin da Jegede ya samu kuri'u 67, sai kuma dan takarar ADC, Prince Adelegan, wanda ya samu kuri'u 6 kacal.

KARANTA: Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS a kasar Ghana

KARANTA: A karshe: Buhari ya fadi dalilin gwamnatinsa na yawan ciyo bashi

Shugaban kwamitin zaben gwajin, Mista Akin Akinbobola, ya ce duk jam'iyyar da ta lashe zaben gwajin ita ce za ta samu nasara ababban zaben da INEC za ta gudanar.

Mista Akinbobola ya taba rike mukamin babban mai bawa tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, shawara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel