Kada ku sake ku zabi Obaseki, dan kama-karya ne - Tinubu ya yi jawabi na musamman

Kada ku sake ku zabi Obaseki, dan kama-karya ne - Tinubu ya yi jawabi na musamman

- Babban jigon jam'iyyar APC na kasa, Tinubu, ya bukaci mutan Edo suyi watsi da gwamnansu

- Jam'iyyar PDP ta zargi Tinubu da kokarin kashe milyan 300 wajen magudin zaben gwamnan jihar

- Tinubu ya yi jawabi ranar Talata amma bai yi martani kan zargin ba

Babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi kira ga al'ummar jihar Edo suyi watsi da gwamna Godwin Obaseki, dake neman zarcewa kan kujerarsa.

A faifan bidiyon da tasahar TVC ta saki, Tinubu ya ce Obaseki ba jarumin demokradiyya bane kuma a yi waje da shi a zaben gwamnan ranar Asabar.

Tinubu na cikin jiga-jigan APC da suka yiwa Obaseki yakin neman zabe a shekarar 2016 karkashin jam'iyyar APC.

Amma daga baya, gwamna Obaseki ya fita daga APC zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bayan rikicin da yaki ci, yaki cinyewa tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar kuma maigidansa, Adams Oshiomole.

A jawabin da Tinubu yayi ranar Talata, Tinubu ya ce Obaseki bai yi gwagwarmayan demokradiyyan Najeriya ba.

"Ina rokonku a matsayina na dan demokradiyya kuma jagora da muyi nazari kan zaben jihar Edo kuma kuyi watsi da Godwin Obaseki," Tinubu Yace.

"Mun sha bakar wahala wajen samar da wannan gwamnati ta demokradiyyar da muke jin dadi yanzu kuma Obaseki bai yi gwagwarmayan tabbatar da demokradiyya a kasa ba."

"Saboda haka, ba zai fahimci daraja da wahalan dake tattare da gwagwarmaya."

"Ya bayyana halinsa na kama-karya, rashin girmama doka, da kuma rashin giramama ku mutanen da kuka zabi yan majalisar amma ya hana rantsar da su."

"A yau, ya dawo ku sake zabenshi. Ina mai rokonku, kuyi watsi da shi kamar yadda yayi watsi da yan majalisa 14."

Kada ku sake ku zabi Obaseki, dan kama-karya ne - Tinubu ya yi jawabi na musamman
Kada ku sake ku zabi Obaseki, dan kama-karya ne - Tinubu ya yi jawabi na musamman
Asali: Twitter

A bangare guda, Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce ta bankado shirin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da wasu manyan APC su ke yi na tafka magudi a zaben Edo.

PDP ta bayyana cewa kusoshin jam’iyyar APC sun tanadi makudan miliyoyin kudi da za su yi amfani da su wajen sayen kuri’ar Bayin Allah a jihar Edo.

A cewar PDP, Bola Ahmed Tinubu sun ware Naira miliyan 300 da za ayi amfani da su domin a saye kuri’a a zaben ranar 19 ga watan Satumban nan.

KU KARANTA: Fasinja 1 ta ji rauni a harin da aka kaiwa jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna

Kakakin yakin zaben jam’iyyar PDP a zaben Edo, Chris Nehikhare, ya ce za a tattaro wadannan miliyoyi ne daga asusun kananan hukumomin Legas.

Nehikhare ya ke cewa kowace karamar hukumar za ta kawo Naira miliyan 15 da za ayi amfani da ita wajen tafka wannan magudi a zaben gwamnan da za ayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel