Farashin kayan masarufi ya tashi da kaso 13.22 a Nigeria

Farashin kayan masarufi ya tashi da kaso 13.22 a Nigeria

- An samu hauhawan farashin kayayyaki a Najeriya da kaso 13.22 a watan Agusta

- Hakan na kunshe ne a alkaluman da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar a ranar Talata

- NBS ta kuma nuna cewa farashin kayan masarufi ya karu da kaso 16% a watan Agusta sabanin kashi 15.48 a watan Yuli

Farashin kayayyaki ya tashi da kaso 13.22 a watan Agusta, ya karu ne daga kaso 12.82 da aka samu a watan Yuli, 2020, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Bisa ga alkaluman da hukumar kididdiga ta kasa wato NBS ta fitar a ranar Talata, 15 ga watan Satumba, ya nuna cewa a kowani wata farashin kaya na ta karuwa, amma na watan Agusta 2020 ya fi yawa da kaso 1.34.

Rahoton ya nuna farashin kayan masarufi ya karu da kaso 16 cikin dari a watan Agusta sabanin kashi 15.48 a watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Da zafinsa: Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun kashe 1 tare da sace mata

Farashin kayan masarufi ya tashi da kaso 13.22 a Nigeria
Farashin kayan masarufi ya tashi da kaso 13.22 a Nigeria
Asali: Original

“Farashin kayan abinci ya karu ne saboda tashin farashin burodi, hatsi, dankali, doya, nama, kifi, kayan marmari na itatuwa, mai da ganyayyaki”, hukumar NBS tayi bayani.

Rahoton ya kara da cewa, dukkannin amfanin gona da ba kayan gwari ba sun karu zuwa kashi 10.52 a watan Agusta daga kashi 10.10 a watan Yuli.

“An samu hauhawar farashin ne a farashin kudin fasinjoji na jiragen sama, asibiti, magunguna, kula da gyaran ababen hawa na kai, kayan gyaran motoci, kudin motar fasinjoji masu tafiyar hanya, gyaran kayan daki da sauransu”, inji rahoton.

KU KARANTA KUMA: Bayan karɓar N5m: Yan bindiga sun kashe jami'in DSS a jihar Katsina

A wani labarin, mun ji cewa an samu raguwar farashin kayayyakin abinci a yankunan karkara da ke jihar Taraba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yankunan da aka samu karyewar farashin kayayyakin sun hada da Mutum Biyu, Garba Chede, Maihula, Dakka, Garbabi, Tella Monkin da kuma Jatau.

An tattaro cewa a yanzu ana sayar da masara sabuwar girbi a kan farashin N8000 a kasuwar Maihula yayin da farashinta ya ke kan N7000 a Dakka.

Hakazalika a kasuwannin Mutum Biyu da kauyan Garba-Chede, ana sayar da buhun masara sabuwar girbi a tsakanin N12,000 da N11,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel