Hoto: 'Yan sanda sun cafke matasa 4 a kan dukan dan sanda har ya mutu

Hoto: 'Yan sanda sun cafke matasa 4 a kan dukan dan sanda har ya mutu

- 'Yan sandan jihar Ogun sun cafke wasu matasa hudu da ake zargi da kashe dan sanda

- Daga cikin wadanda aka kaman akwai direban babbar mota wanda suka yi hayaniya da dan sandan

- Sun lakada masa duka bayan ya yi musu magana a kan tukin ganganci da suke yi amma sai suka kama shi da duka

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wasu matasa hudu a kan zarginsu da ake da lakadawa wani dan sanda mugun duka har ya mutu.

Sun yi babbar aika-aikar a yankin Dalemo da ke Sango, karamar hukumar Ado-Odo-Ota ta jihar a ranar Lahadi, 13 ga watan Satumba.

A wata takardar da aka saki a ranar Litinin, 14 ga watan Satumba, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce mutum hudun wani direba ne yayi hayarsu domin yi wa dan sandan duka saboda wani rikici ya hada su.

Sunayen wadanda suka yi a aika-aikar su ne: Jelili Ismaila mai shekaru 22; Amidu Bankole mai shekaru 34; Elijah Samson mais shekaru 36; da Moses Proboye, mai shekaru 34.

Oyeyemi ya ce, mamacin yana da mukamin constable kuma suna raka wani babba ne daga Idah a jihar Kogi zuwa Legas lokacin da lamarin ya faru.

KU KARANTA: Ba ajinmu daya ba, digiri gareni shi kuwa mijina mai walda ne - Matar aure ta sanar da kotu

Hoto: 'Yan sanda sun cafke matasa 4 a kan dukan dan sanda har ya mutu
Hoto: 'Yan sanda sun cafke matasa 4 a kan dukan dan sanda har ya mutu. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Duba kyawawan hotunan katafaran gidajen fitattun 'yan Najeriya 8

"Binciken farko ya bayyana cewa mamacin dan sandan da wani dan sandan suna raka ogansu zuwa Idah ne ta jihar Kogi daga Legas.

"A kan hanyarsu ta a Sango Ota, wani matukin babbar mota mai suna Jelili Ismaila, ya yi tukin ganganci inda ya kusa ture musu mota.

"A yayin kokarin kauce musu, babbar motar ta fada wani rami wanda yayi sanadin facin tayar motar.

"Hakan yasa 'yan sandan biyu suka sauko tare da jan kunnen matukin babbar motar. Amma sai direban ya daura laifin a kansu inda ya kira 'yan daba suka hau dukan 'yan sandan har daya ya mutu," takardar tace.

Bayan gano cewa sun kashe dan sandan, direban da 'yan dabansa sun tsere. Amma kuma 'yan sanda sun bi su inda suka damkesu a maboyarsu.

A halin yanzu, gawar marigayin dan sandan tana ma'adanar gawawwaki na babban asibitin Ota.

Oyeyemi ya kara da cewa 'yan sanda sun cigaba da neman sauran wadanda ake zargi, shafin Linda Ikeji ya bayyana.

Awani labari na daban, wata kotun majistare da ke zama a Osogbo da ke jihar Osun ta gurfanar da wata mata mai suna Florence Samuel a ranar Juma'a, sakamakon zarginta da ake da dukan 'yar sanda mai mukamin sajan, Caroline Olaitan.

Florence mai shekaru 28 tana siyar da burkutu a wani shago da ke yankin Balogun Agoro a Osogbo. An zargeta da dukan 'yar sandan tare da hana a kamata bayan Caroline da ziyarci shagonta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel