La-liga: Ali Nuhu ya zama Jakadan kwallon kafa a Arewacin Najeriya
- Sanannen jarumin Kannywood, Ali Nuhu, ya zama jakadan La Liga a arewacin Najeriya
- Hakan ya bayyana ne a taron farko da masoyan La Liga suka yi a Kano
- Jarumin ya tabbatar da cewa zai samar da alaka mai karfi a yayin da yake jakadan La Liga
Fitaccen jarumin masana'antar fina-finan Hausa, furodusa kuma mai bada umarni, Ali Nuhu, ya bayyana a matsayin jakadan La Liga na arewacin Najeriya.
An bayyana jarumin a wannan matsayin a yayin taron farko na masoya La Liga na arewa wanda gidan rediyon Arewa da La Liga suka dauka nauyi a Kano.
Ali Nuhu ya tabbatar wa da masoyan La Liga na yankin arewacin Najeriya da cewa zai samar da alaka mai karfi kuma mai cike da zaman lafiya a yayin da ya zama jakaden La Liga a arewa.
Hakazalika, shugaban fannin labaran wasanni na gidan rediyon Arewa, Sherif Abdallah, ya ce Kano ita ce gidan La Liga, Daily Trust ta wallafa.
Ya kara da cewa, wannan taron na farko shine zai zamanto tushen dukkan ababen arzikin da za su shigo kasar nan da arewa.
"Mun kawo La Liga kusa da masoyanta, mun kaddamar da ita a kusa. Ba za mu yi kasa a guiwa ba wurin ci gaba da karfafa alakarta da masoyanta a Najeriya," Abdallah yace.
A yayin jawabi a taron, jakadan La Liga na Najeriya, Mutiu Adepoju ya nuna jin dadinsa a kan yadda suka samu masoya a Kano da sauran sassan arewacin Najeriya.
KU KARANTA: Edo 2020: Yadda wanda na gada ya dinga rantowa jihar kudi yana watanda da su - Obaseki
KU KARANTA: Baka damu da mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki ba - Kungiyoyi a Kano sun caccaki Buhari
A wani labari na daban, shahararren jarumin fina-finai, Ali Nuhu ya ce hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) za ta yi masa gwajin cutar coronavirus.
Jarumi Ali Nuhu tare da wasu 'yan Kannywood biyar na daga cikin taurarin da suka samu halartar bikin karrama jarumai da aka gudanar a Legas a ranar Asabar 14 ga watan Maris 2020.
Gwamnatin jihar Legas ta yi kira ga duk wandanda suka halarci bikin da su je a yi musu gwajin cutar coronavirus saboda an gano cewa akwai mai dauke da cutar cikin wadanda suka halarci bikin. A hirar da fitaccen jarumi.
Ali Nuhu ya yi hira da BBC a daren yau Talata, ya ce jami'an hukumar NCDC sun samesa inda suka bukaci da ya bi su ofishinsu don yi masa gwajin cutar coronavirus.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng