Wammako: Babu ruwan rigar mutuwa da shekarun mutum inji Shugaba Buhari

Wammako: Babu ruwan rigar mutuwa da shekarun mutum inji Shugaba Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa Aliyu M. Wammako ta’aziyya

- Sanatan jihar Sokoto, Aliyu Wammako ya rasa diyarsa yayin da ta je haihuwa

- Kafin wannan lokaci, irinsu Atiku Abubakar da wasunsu sun aika ta’aziyyarsu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fito ya yi magana game da mutuwar Sadiya Aliyu Magatakarda Wamakko.

Idan za ku iya tunawa, Marigayiya Aliyu Magatakarda Wamakko ta rasu ne a wajen haihuwa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun bakinsa, Malam Garba Shehu.

Kamar yadda Garba Shehu ya bayyana a ranar 13 ga watan Satumba, 2020, shugaban kasar ya yi takaicin wannan rashi da aka yi.

KU KARANTA: 'Danuwan tsohon Gwamna Wammako ya rasu

Shugaban Najeriyar ya nuna takaicinsa da bakin ciki game da wannan rashi da tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya yi.

“Mutuwar diyar Wammako ta zo mani da ban mamaki, zuciyata da addu’a ta, ta na ga Sanata Wammako da iyalinsa.”

Wammako: Babu ruwan rigar mutuwa da shekaru mutum inji Shugaba Buhari
Sadiya Wammako Hoto: Linda Ikeji
Source: Twitter

Muhammadu Buhari ya ce, “mutuwa babu ruwanta da shekaru, rashin wannan karamar mata a tsakiyar ganiyar shekarunta, abin tausayi ne.”

Buhari ya ce ya san halin da Sanatan na Sokoto ya ke ciki.

KU KARANTA: Diyar Sanatan Sokoto, Wammako ta cika a asibitin UDTH

“Ina rokon Allah ya ba shi hakurin juriya da wannan babban rashin da ‘diyar cikinsa.”

Jawabin shugaban kasar ya kare da cewa: “Allah ya yi mata rahama, ya ba ta Aljanna.”

Sadiya Aliyu Magatakarda Wamakko ta rasu ne wajen haihuwa ta na shekaru 23. A musulunci ana sa ran cewa wanda ta mutu wajen nakuda, ta yi mutuwar shahada.

Shi kansa shugaba Muhammadu Buhari ya taba rasa diyarsa a 2012. Babbar ‘diyar shugaban kasar, Zulaihat Buhari ta rasu ne a 2012 a sakamakon ciwon sikila.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel