Bidiyon wajen da aka binne marigayi Sanata Ajimobi da aka cika wajen da kayan alatu, da wutar lantarki wacce bata daukewa
- 'Yan Najeriya sun nuna rashin jin dadinsu akan wajen da aka binne tsohon gwamna Abiola Ajimobi
- Wajen da aka binne tsohon dan siyasar an gina shi kamar daki ne, inda aka sanya na'urar sanyaya daki aka kuma samar da wutar lantarki da bata daukewa
- Wasu 'yan Najeriya sunyi Allah wadai da wannan abu, inda wasu kuma suka bayyana cewa abinda danginshi suke so kenan
'Yan Najeriya sun hau shafukan sadarwa domin nuna rashin jin dadinsu akan bidiyon dake yawo dake nuni da wajen da aka binne tsohon gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi.
A wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa, an nuno wajen da aka binne tsohon sanatan wanda aka gina shi kamar daki aka sanya duk wasu abubuwa da mutum yake bukata na rayuwa
A cikin dakin an sanya na'urar sanyaya daki, da kuma wutar lantarki wacce bata daukewa.
Mutane dai sunyi ta tofa albarkacin bakinsu akan wannan abu.
KU KARANTA: Budurwa ta rayu bayan ta fado daga bene mai hawa 8, yayin da take gujewa saurayinta
Wani mai suna @Omarigbebi a shafin Twitter cewa yayi marigayin da Allah ya bashi lada da ace wajen an mayar da shi wajen koyon karatun Qur'ani.
Ya ce: "Inda sun mayar da wannan karamin wajen ya zama Masallaci ko makarantar Islamiyya, da ladan abinda ake yi a wajen ya dinga bin shi kenan har zuwa karshen duniya. Allah yasa abinda muka mutu muka bari ya zama alkhairi a gare mu, Ameen. Allah ya jikanka ya kuma saka maka da Aljannah Firdausi Ajimobi."
Shi kuwa @AdeElegbede cewa yayi: "Haka 'yan uwanshi suka so mishi. Ya mutu ya tafi kuma. Ku nemo mafita akan karin kudin wutar lantarki dana man fetur."
Wani kuwa cewa yayi: "Ina tantamar idan har shine zai bari ayi masa wannan abu da aka yi."
Idan ba a manta ba Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda matar tsohon gwamnan Florence Ajimobi bayan mutuwarsa ta bayyana cewa tsohon mijin nata yayi rayuwa mai kyau.
Matar marigayin ta bayyana hakane a lokacin da shugabannin 'yan jarida na jihar Oyo suka kai musu ziyarar barka da sallah, karkashin jagorancin shugabansu Ademola Babalola.
KU KARANTA: Zamfara: Jiragen yaki sun ragargaza sansanin 'yan bindiga, da yawa sun rasa rayukansu
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng