Zamfara: Jiragen yaki sun ragargaza sansanin 'yan bindiga, da yawa sun rasa rayukansu

Zamfara: Jiragen yaki sun ragargaza sansanin 'yan bindiga, da yawa sun rasa rayukansu

- Hukumar sojin Najeriya ta sanar da yadda ta ragargaza sansanin 'yan bindiga da ke dajin Doumborou a jihar Zamfara

- Manjo janar John Enenche ya sanar da cewa, sun samu wanann damar ne bayan bayanan sirri da suka samu na sabon sansanin

- Wannan lamarin ya yi sanadin ragargaza kayan aiki da makaman 'yan bindigar da ke dajin

Da yawa daga cikin 'yan bindiga daga kungiyar fitaccen dan bindiga 'Dangote' sun rasu sakamakon ruwan wutar da dakarun sojin Operation Lafiya Dole suka yi musu ta jiragen yaki.

Kamar yadda takardar ta sanar, shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo janar John Enenche, ya ce an yi wannan ragargazar ne bayan bayanan sirri da aka kai wa sojojin a kan cewa Dangote ya kafa sabon sansani a dajin Doumborou da ke Zamfara.

Takardar ta ce, "Rundunar Hadarin Daji ta ragargaza wani sansanin 'yan bindiga da ke dajin Daumborou ta jihar Zamfara.

"Ragargazar da aka yi a ranar 13 ga watan Satumban 2020 na daga cikin sabon atisayen Wutan Daji 2, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar 'yan bindiga masu yawa."

Ya kara da cewa, a sakamakon harin, an samu damar tarwatsa ma'adanar makaman 'yan bindigar a sabon sansanin da ke dajin. Hakan babbar nasara ce a kan yakin da ake da ta'addanci a arewa.

KU KARANTA: Saurayi ya tura wa budurwa N50,000 saboda damar hira da ita da ta bashi a kafar sada zumunta

Zamfara: Jiragen yaki sun ragargaza sansanin 'yan bindiga, da yawa sun rasa rayukansu

Zamfara: Jiragen yaki sun ragargaza sansanin 'yan bindiga, da yawa sun rasa rayukansu. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Motar haya dauke da fasinjoji ta ci karo da jirgin kasa

A wani labari na daban, shugaban kwamitin kula da rundunar sojin Najeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume, na jam'iyyar APC da ke wakiltar jihar Borno ta Kudu, ya jinjinawa kokarin rundunar sojin Najeriya.

Ya sanar da cewa, suna iyakar kokarinsu wurin yaki da rashin tsaro a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabas na kasar nan, inda mayakan ta'addanci suka yi katutu.

Ndume wanda ya tabbatar da cewa rundunar sojin bayan yaki da rashin tsaro suna kokarin tabbatar da ganin dawowar 'yan gudun hijira zuwa gidajensu a Borno.

Ya sanar da yadda sojojin suke kokarin samar da kayan rage radadi ga mazauna yankin domin ganin sun koma rayuwarsu kamar yadda suke a da kafin kafuwar ta'addanci.

Tsohon shugaban majalisar ya sanar da cewa, bai dade da dawowa daga zagayen mazabarsa, ya ce rundunar sojin ta cancanci jinjina a kan yadda tsaro yake tabbata na rayuka da kadarori.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel