Duba kyawawan hotunan katafaran gidajen fitattun 'yan Najeriya 8

Duba kyawawan hotunan katafaran gidajen fitattun 'yan Najeriya 8

- Zama fitacce a kasar nan yana tafe da manyan kalubale masu tarin yawa

- Sau da yawa fitattu a kasar nan kan gina katafaran gidaje wadanda ke zama sha kallo

- Manyan fitattu a Najeriya da suka mallaki manyan gidaje yawanci jarumai ne ko mawaka

Zama fitacce a Najeriya na da matukar muhimmanci kuma abun alfahari ne. Amma kuma dole ne ya zamanto mutum na iya siyan wasu kayan kyale-kyale tare da kayan kece raini.

A nahiyar Afrika, ballantana a kasar Najeriya, mutum na iya bayyana arzikinsa ta hanyar mallakar katafaren gida.

Wasu daga cikin fitattun 'yan Najeriya sun shiga cikin tsararraki, inda suka siya gidajen wuce tsara, lamarin da yasa jama'a da yawa suke sha'awarsu.

A yau, za mu duba yadda katafaren gidajen wasu fitattun 'yan Najeriya suke kamar yadda suka bayyana a kafafen sada zumuntar zamani.

1. . Iyabo Ojo: Tsohuwar jarumar fina-finan kudancin Najeriya, Iyabo Ojo ta bayyana hotunan sabon katafaren gidanta da ke yankin high-brow a Lekki da ke Legas.

KU KARANTA: Yaki da 'yan bindiga: Sojin Najeriya sun ceto mutum 32, sun damke 'yan bindiga 26

2. Bimbo and Okiki Afolayan: A shekarar da ta gabata, fitattun jaruman fina-finan Nollywood Bimbo da Okiki Afolayan, sun bayyana sabon katafaren gidansu a kafar sada zumuntar zamani.

3. Mercy Aigbe: A wani lokaci a shekarar 2018, jaruma Mercy Aigbe ta zama mamallakiyar wani katafaren gida. Jarumar ta dinga samun sakonnin sam barka daga masoyanta.

KU KARANTA: Ba ajinmu daya ba, digiri gareni shi kuwa mijina mai walda ne - Matar aure ta sanar da kotu

4. Toke Makinwa: Wannan fitacciyar jarumar ta zama abun kwatance a 2018 bayan siyan katafaren gidanta.

Kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar, Toke ta siya gidan da ke Banana Island da kudin da ya kai miliyan 260.

5. Bobrisky: Fitaccen mata-maza mai suna Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky, yana daya daga cikin fitattu a kasar nan. Gidansa kuwa ya kasance abun kwatance ga jama'a.

6. Peter Okoye: Mawaki Peter Okoye wanda yake daya daga cikin 'yan kungiyar PSquare yana daga cikin fitattun da gidansu ya zama abun kallo.

Mawakain ya kan wallafa hotunan katafaren gidansa lokaci zuwa lokaci a shafinsa na Instagram.

7. Paul Okoye: Paul Okoye, daya daga cikin 'yan kungiyar PSquare ya cigaba da zama sha kallo a wurin masoyansa da kyawawan hotunan katafaren gidansa.

8. Davido: Fitaccen mawaki Davido cikin kwanakin nan ya mallaki katon gida a Banana Island a Legas. Ya wallafa kyawawan hotunan gidansa a kafafen sada zumuntar zamani.

A wani labari na daban, katafaren gidan mawakiya Rihanna da ke birnin London wanda ta kwashe kusan shekaru biyu da rabi ana gina shi an daga shi domin siyarwa, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Za a siyar da katafaren gidan a kan pam miliyan 32 wanda yayi daida da Naira biliyan 14, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Gidan mai dakin kwana takwas yana nan a St Johns, yana da kofofi biyar manya tare dakin wanka mai kamar wurin gyaran jiki tare da katafaren lambu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel