Salami ya kori lauyoyin Magu yayin zaman kwamitin bincike
- A ranar Litinin ne kwamitin da ke binciken tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya sake zama
- Shugaban kwamitin, Ayo Salami, ya umarci jami'an tsaro su fitar da wasu daga cikin lauyoyin Magu daga dakin da kwamitin ke zama
- Ayo Salami, tsohon shugaban kotunan daukaka kara da Goodluck Jonathan ya yi wa ritayar dole daga aiki, ya ce lauya daya ne su ka amince zai kare Magu
An dan samu yamutsi bayan shugaban kwamitin bincike, Ayo Salami, ya umarci wasu lauyoyin Magu su fice daga dakin da da kwamitin ke zamansa a fadar shugaban kasa.
Ayo Salami ne shugaban kwamitin bincike da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa domin bankado cin hanci da kwato kadarorin gwamnati.
Salami ya umarci jami'an tsaro su fita da wasu lauyoyin Magu guda biyu; Zainab Abiola da Aliyu Lemu, jim kadan bayan gabatar dasu.
An fara samun matsala ne bayan Wahab Shitu, shugaban tawagar lauyoyin Magu, ya mike domin gabatar da sauran abokan aikinsa.
Sai dai, Salami ya katsewa Shittu hanzari ta hanyar sanar da shi cewa shine kadai za a bari ya kare Magu.
Bayan hakan ne sai ya umarci jami'an tsaro su fitar da sauran lauyoyin.
A ranar Laraba, 15 ga watan Yuli, aka saki Magu bayan ya shafe sati biyu a tsare a hedikwatar rundunar 'yan sanda.
Magu ya fara gurfana a gaban kwamiti bincike a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, kuma tun daga ranar wasu jami'an 'yan sanda su ka yi awon gaba da shi zuwa hedikwatarsu.
DUBA WANNAN: Amfani da illolin lemon tsami ga lafiyar maniyyin mutum musamman maza
DUBA WANNAN: COVID-19: Sabon Matakin da gwamnatin Saudiya ta dauka kan rufe iyakoki da sufurin jiragen sama
An fara binciken Magu ne bisa zarginsa da almundahana da kuma rashin biyayya, kamar yadda ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rubuta korafi a kansa zuwa fadar shugaban kasa.
Har yanzu kwamitin Salami ya na cigaba da gudanar da bincike a kan Magu duk da an bayar da shi beli.
Shugaba Buhari ya kafa kwamitin ne domin gudanar da bincike tare da kwato kadarorin gwamnati daga hannun wasu manyan jami'an gwamnati; na baya da na yanzu, da ake zargi da almundahana, waskiya, ko sama da fadin kudi, dukiya ko wata kadara mallakar gwamnati.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng