Bude boda: Ku ci abinda kuka shuka - Sakon Buhari ga ƴan Nigeria

Bude boda: Ku ci abinda kuka shuka - Sakon Buhari ga ƴan Nigeria

- Shugaban kasa Buhari ya yi watsi da tsammanin mutane na cewa za a bude iyakokin Najeriya kwanan nan

- Buhari ya bayyana hakan a lokacin wani rangadi na ganin barnar da ambaliyar ruwa yayi a jihar Kebbi

- Shugaban kasar ya samu wakilcin ministan noma a yayin rangadin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karshen mako, ya ce gwamnatinsa bata shirya bude iyakokin kasar ba a yanzu.

Shugaban kasar ya bukaci yan Najeriya da su ci abunda ake shukawa a kasar.

Ya fadin hakan ne da yake amsa tambayoyi a filin Jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi a lokacin wani rangadi don ganin irin barnar da ambaliyar ruwa ya yi a jihar Kebbi.

Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin ministan noma, Mohammed Sabo Nanono, ya ce a shirye gwamnatin tarayya take ta ba manoma tallafi domin bunkasa harkar noma.

Bude boda: Ku ci abinda kuka shuka - Sakon Buhari ga ƴan Nigeria
Bude boda: Ku ci abinda kuka shuka - Sakon Buhari ga ƴan Nigeria
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa noman shinkafa da ake yi a jihohin Neja, Taraba, Jigawa da Kebbi kadai zai iya ciyar da kasar gaba daya inda ya dasa ayar tambaya: “toh menene na shigo da abinci alhalin za mu iya samar da shi?”

Buhari ya ba mutane tabbacin basu tallafi a lokacin noman rani da bayanta.

A nashi bangaren ministan ya bayyana cewa: “shugaban kasa ya turo ni domin nazo na ga irin barnar da aka samu a jihar Kebbi. Kuma na gani. Za mu rage wa yan Kebbi radadi fiye da sauran jihohin.”

Ya gargadi wadanda abun ya shafa a kan kada su yanke kauna, inda ya kara da cewar gwamnati mai ci za ta farfado dasu, cewa ma’aikatarsa na hada kai da takwaranta na agaji don basu kayan tallafi.

A wani labari na daban, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya umarci babban bankin kasa (CBN) da ya daina bayar da tallafin canjin kudi ga masu kasuwancin shigo da abinci cikin Najeriya.

A wani jawabi Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari, ya fitar, ya ce shugaban kasa ya bayar da wannan umarni ne domin inganta cinikin kayan abincin da aka noma a cikin gida.

Da yake karbar bakuncin manyan 'ya'yan jam'iyyar APC a gidansa na garin Daura, shugaba Buhari ya ce gwamnati zata yi amfani da kudin tallafa wa masu shigo da kayan abinci wajen inganta tattalin arziki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel