Yaki da 'yan bindiga: Sojin Najeriya sun ceto mutum 32, sun damke 'yan bindiga 26

Yaki da 'yan bindiga: Sojin Najeriya sun ceto mutum 32, sun damke 'yan bindiga 26

- Daga cikin kokarin zakakuran sojin Najeriya, rundunar Operation Sahel Sanity ta ceto mutum 32 da aka yi garkuwa da su

- Mukaddashin daraktan yada labarai na OSS, Birgediya janar Benard Onyeuko ya ce sun kashe 'yan bindiga 26

- Ya tabbatar da cewa sun samo shanun sata daga hannun 'yan bindiga har 150, kuma sun bai wa mamallakansu

A kokarin ganin bayan 'yan bindiga da suka addabi yankin arewa maso yamma, rundunar Operation Sahel Sanity, ta ceto mutum 32 da aka yi garkuwa da su.

Ta cafke 'yan bindiga 26, masu hada kai da su, samar musu da makami da miyagun kwayoyi bayan musayar wuta da suka yi.

A wannan musayar wutar, biyu daga cikin 'yan bindigar sun rasa rayukansu, Vanguard ta wallafa.

Mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar sojin, Birgediya Janar Benard Onyeuko,wanda ya fitar da sanarwar, ya ce an samu shanun sata har 150 bayan artabun.

Ya ce, "A ranar 30 ga wata Augustan 2020, bayan bayanan sirri da aka samu a kan kaiwa da kawowar 'yan bindiga da shanu 40, zakakuran sojin sun kai samame inda suka taresu a babban titin Anka zuwa Gummi.

"Amma kuma, bayan 'yan bindigar sun hango dakarun sojin daga nesa, sun tsere tare da barin shanun inda suka fada daji. An yi nasarar samun dukkan shanun kuma an mika su ga masu shi.

KU KARANTA: Yan sanda sun kama wani da yayi fim din batsa da kayan mabiya wani addinin gargajiya a Ogun

Yaki da 'yan bindiga: Sojin Najeriya sun ceto mutum 32, sun damke 'yan bindiga 26

Yaki da 'yan bindiga: Sojin Najeriya sun ceto mutum 32, sun damke 'yan bindiga 26. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KARANTA: Zamfara: 'Yan jam'iyyar APC sun tada zanga-zanga a kan kama shugabansu

"A wani cigaba makamancin hakan, a ranar 31 ga watan Augustan 2020, dakarun da ke sintiri sun sake kama wasu da ake zargin masu satar shanu ne a kauyen Zango da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

"'Yan bindigar sun shiga kauyen tare da sace shanu amma isar dakarun yasa suka gudu tare da fadawa daji. Dukkan shanun an mika su ga masu shi."

"A wani cigaba, a ranar 1 ga watan Satumban 2020, dakarun da ke yankin Faskari ta jihar Kastina sun cafke wasu 'yan bindiga yayin da suke sintiri tare da wasu mata biyu da suka yi garkuwa da su.

"A yayin da sojin suka tunkari 'yan bindigar, sun tsere tare da fadawa cikin tsaunika," takardar tace.

A wani labarin na daban, shugaban kwamitin kula da rundunar sojin Najeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume, na jam'iyyar APC da ke wakiltar jihar Borno ta Kudu, ya jinjinawa kokarin rundunar sojin Najeriya.

Ya sanar da cewa, suna iyakar kokarinsu wurin yaki da rashin tsaro a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabas na kasar nan, inda mayakan ta'addanci suka yi katutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel