Ba ajinmu daya ba, digiri gareni shi kuwa mijina mai walda ne - Matar aure ta sanar da kotu

Ba ajinmu daya ba, digiri gareni shi kuwa mijina mai walda ne - Matar aure ta sanar da kotu

- Wata matar aure mai suna Sadiat Abbas ta gurfana a gaban wata kotun gargajiya inda ta bukaci a rabata da mijinta

- Kamar yadda ta sanar a gaban alkali, ta ce digiri gareta yayin da mijinta ke aikin walda, hakan yasa suka zama ba aji daya ba

- Ta zargi mijinta da saka mata karfi tare da tilasta ta idan zai sadu da ita, lamarin da tace yana ci mata tuwo a kwarya

Wata matar aure ta gurafana a gaban kotu inda ta bukaci da a tsinke igiyar aurenta da mijinta mai sana'ar walda, jaridar The Nation ta wallafa.

"Digiri gareni yayin da yake aikin walda. Kuskure nayi na samu ciki tare da shi kuma hakan yasa bani da wani zabi da yawuce in auresa.

"Auren da shi babu dadin zama saboda ba ajinmu daya ba. Ya taba sace min dan kamfai wanda nake tunanin zai kai ne a yi masa sihiri," Matar aure ta sanar da alkali.

Amma maigidan nata ya yi martani da cewa, "Bata mutunta ni kuma ita ke fadin lokutan da zan sadu da ita. Na saba yawon zuwa gidajen abinci saboda bata yi min girki. Sai karfe 11 na dare take dawowa daga aiki."

Wata mata mai suna Sadiat Abbas ta mika bukatar tsinke igiyar aurenta da mijinta mai suna Lasisi Abbas, a gaban wata kotun gargajiya da ke Oja Oba a garin Ibadan na jihar Oyo.

A korafin Sadiat, ta ce mijinta baya daukar dawainiyarsa ta magidanci kuma yana mata ta karfi wurin saduwa. Akwai lokacin da ya taba satar dan kamfanta domin kai wa boka.

Mai karar ta ce daga baya watsa mata kayanta yayi waje, inda yayi ikirarin zai watsa mata acid a fuska.

Babu ja'in'ja Lasisi ya amince da bukatar sakin a gaban kotun.

Amma kuma, wanda ake karar ya musanta dukkan zargin da matarsa ta bayyana, inda yace ta shirya su ne domin alkali ya bata gaskiya.

KU KARANTA: Hotunan cikin katafaren gidan Rihanna na London wanda za a siyar a 14 biliyan

Ba ajinmu daya ba, digiri gareni shi kuwa mijina mai walda ne - Matar aure ta sanar da kotu

Ba ajinmu daya ba, digiri gareni shi kuwa mijina mai walda ne - Matar aure ta sanar da kotu. Hoto daga The Nation
Source: Getty Images

KU KARANTA: Dalilinmu na yin taro da Obasanjo, Afenifere da sauransu - Dattawan arewa

Lassisi ya bayyana cewa, mai korafin ta saba cin mutuncinsa kuma da kanta ta sa yake mata tilas idan zai sadu da ita.

Kamar yadda yace, mai korafin ta taba kona shi da dutsen guga, saboda ya ce dole sai ya sadu da ita. Ya kara da cewa ta bar gidansa da kanta ba tare da ya ce mata komai ba.

A yayin yanke hukunci bayan jin ta bakin dukkan ma'auratan, Alkali Ademola Odunade ya ce dole ne kotun ta tsinke igiyar auren saboda tashin hankalin da ya bayyana.

Odunade ya yanke hukuncin raba ma'auratan tare da bai wa Sadiat rikon dan da suka haifa.

An bukaci wanda ake karar da ya dauka dawainiyar yaron, iliminsa da kuma lafiyarsa su zama abin fifitawa.

Kamar yadda Odunade yace, dole ne Lasisi ya dinga bai wa Sadiat N5,000 a kowanne wata domin ciyar da dansa.

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Ladidi Abbas, a ranar Talata ta maka mijinta mai suna Shehu Abbas a gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke zama a Magajin Gari, a Kaduna.

Ladidi ta bukaci mijinta da ya sauwake mata igiyoyin aurensa, saboda dukan da take sha a hannunsa a duk lokacin da suka samu matsala, jaridar The Nation ta wallafa.

Kamar yadda tace, an kwantar da ita a asibiti na tsawon kwanaki 13 a wancan dukan da yayi mata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel