Yanzu-yanzu: Motar haya dauke da fasinjoji ta ci karo da jirgin kasa

Yanzu-yanzu: Motar haya dauke da fasinjoji ta ci karo da jirgin kasa

- Wata mota dauke da fasinjoji guda shida ta yi karo da jirgin kasa

- Lamarin ya auku a yankin Oshodi da ke jihar Legas

- Shugaban LASEMA a jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da aukuwar lamarin

Wata mota dauke da fasinjoji har shida ta ci karo da jirgin kasa da ke tafiya dauke da fasinjoji a Oshodi da ke jihar Legas.

Darakta janar na hukumar taimakon gaggawa (LASEMA), Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce motar hayan ta haye dogon, inda ta ci karo da jirgin mai tafiya, gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito.

Wani matashi mai shekaru 20 ya rasu a ranar Litinin yayin da wasu bakwai suka samu miyagun raunila bayan motar haya ta ci karo da jirgin kasa.

An gano cewa, motar hayan mai lamba GGE972GE tana da fasinjoji shida yayin da dayar motar ke dauke da mutum biyu, sannan suka fada dogon a kokarinsu na gujewa cunkoson ababen hawa.

KU KARANTA: A karon farko an rubuta jarrabawar WAEC a garin Chibok shekaru 6 bayan sace dalibai mata da Boko Haram suka yi a garin

Yanzu-yanzu: Motar haya dauke da fasinjoji ta ci karo da jirgin kasa
Yanzu-yanzu: Motar haya dauke da fasinjoji ta ci karo da jirgin kasa. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

KU KARANTA: Sai muna kwance ni da ita sai ta sulale zuwa dakin wani gardi suyi iskanci - Malamin Islamiyya ya kai matar shi kara kotu

A rashin sanin ababen hawan, sauran masu ababen hawan sun tsaya domin bai wa jirgin kasa damar wucewa kafin su wuce.

Ma'aikatan gaggawa da suka gaggauta zuwa wurin hatsarin sun ciro dukkan mutum takwas din da ke cikin ababen hawan, jaridar The Nation ta wallafa.

Kamar yadda Darakta janar na LASEMA ya sanar, ya shawarci masu ababen hawa da su dinga hakuri yayin cunkoso a kan tituna.

A wani labari na daban, mutum 14 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da mutum 8 suka samu raunika daban-daban sakamakon hatsarin da aka yi kusa da kauyen Makole da ke kan titin Wudil zuwa Kano a jihar Kano.

Kwamandan yankin na hukumar kiyaye hadurra na jihar Kano, Zubairu Mato ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya aika wa jaridar Daily Trust a ranar Juma'a.

Zubairu ya ce hatsarin ya faru wajen karfe 10:40 na daren a ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel