Jerin jihohi 28 da za su fuskanci ruwan sama mai tsanani kafin karshen 2020

Jerin jihohi 28 da za su fuskanci ruwan sama mai tsanani kafin karshen 2020

- Gwamnatin Najeriya ta ja hankalin jama'a a kan ruwan sama kamar da bakin kwarya da za a fuskanta a wasu jihohi 28 kafin karshen 2020

- Ministar walwala da jin dadin al'umma, Sadiya Umar Farouq ce ta yi wannan jan hankali cikin wata sanarwa da aka fitar

- Sadiya ta yi kira ga gwamnatocin jiha a kan su dauki matakan hana barkewar annoba ta sanadiyar ruwan saman da kuma ambaliyar ruwa

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jihohi 28 na kasar za su fuskanci matsanancin ruwan sama kafin karshen shekarar nan, jaridar The Cable ta ruwaito.

A wani jawabi, Sadiya Umar Farouq, ministar walwala da jin dadin al’umma ta bukaci gwamnatocin jiha da su dauki matakan magance barnar ruwan saman da ambaliyar ruwa.

Ta ce mahangar ambaliyar ruwa na 2020 ya yi hasashen cewa kananan hukumomi 102 a jihohin kasar 28 za su fuskanci matsanancin ruwan sama, yayinda kananan hukumomi 275 a jihohi 36 da Abuja za su fuskanci matsakaicin ambaliyar ruwa.

KU KARANTA KUMA: Wani mutum ya kashe gwaggonsa mai shekaru 60 da hannunsa

Jerin jihohi 28 da za su fuskanci ruwan sama mai tsanani kafin karshen 2020

Jerin jihohi 28 da za su fuskanci ruwan sama mai tsanani kafin karshen 2020 Hoto: The Cable
Source: UGC

Ministar ta yi kira ga hukumomin bayar da agajin gaggawa na jiha, hukumomin kananan hukuma da sauran hukumomin agaji da su dauki matakan kiyayewa ta hanyar wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da barin hanyar da ruwa zai bi.

Ta bayyana jihohin da za su fuskanci matsanancin ruwan sama da yiwuwar ambaliyar ruwa kamar haka:

1.Borno

2. Yobe

3. Gombe

4. Adamawa

5. Taraba

6. Bauchi

7. Plateau

8. Nasarawa

9. Benue

10. Niger

11. Kogi

12. Enugu

13. Anambra

14. Imo

15. Abia

16. Rivers

17. Akwa Ibom

18. Delta

19. Edo

20. Ekiti

21. Osun

22. Kwara

23. Zamfara

24. Sokoto

25. Lagos

26. Ondo

27. Bayelsa

28. Kaduna

KU KARANTA KUMA: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki

A wani labari na daban, mun ji cewa yan gida daya su shida da suka hada da uba, matarsa da yaransu hudu sun mutu.

Mummunan al’amarin ya afku ne sakamakon rushewar gidan da suke ciki a yankin Yaldu da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.

A bisa ga rahotanni, ginin ya zube ne bayan shafe tsawon kwanaki da dama ana zuba ruwan sama a yankin.

Iyalan wadanda ke cikin gidan a lokacin da ya rushe duk sun mutu, shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel